Zaben 2019: Hukumar NYSC zata baiwa INEC matasa 20,000 don zama jami'an zabe

Zaben 2019: Hukumar NYSC zata baiwa INEC matasa 20,000 don zama jami'an zabe

- NYSC a jihar Legas, ta bayyana cewa zata gabatarwa INEC sunayen matasa 20,000 da ke yiwa kasa hidima, don sanyasu a matsayin jami'an INEC a zaben 2019

- NYSC ta ce matasan sun samu horo daga INEC kan yadda zaben zai gudana da kuma yadda zasuyi amfani da na'urar tantance masu kada kur'a

- Kodinetan hukumar a jihar Legas, Momoh, ya ce tabbatar d cewa akwai kwamitin kula da tsaro a zaben, wanda ya sanya matakai don kare lafiya da rayukan mambobin NYSC a zaben

Hukumar dake kula da matasa masuyiwa kasa hidima NYSC a jihar Legas, ta bayyana cewa zata gabatarwa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC sunayen matasa 20,000 da ke yiwa kasa hidima a yanzu a ranar 6 ga watan Disamba, don sanyasu a matsayin jami'an INEC a zaben 2019.

Mr. Mohammed Momoh, kodinetan NYSC na jihar Legas, ya shaidawa manema labarai a ranar Laraba a wajen rufe taron yaye matasa masuyiwa kasa hidima na 2018, a gurbin 'C' zango na II, a sansanin NYSC dake Iyana-Ipaja, jihar Legas.

Momoh ya ce a yanzu haka, akwai mambobin NYSC 19,000 da ke yin hidima a jihar wadanda za a gabatarwa INEC kuma zasu yi aikin zaben 2019.

KARANTA WANNAN: Majalisar wakilai ta janye kudurin dokar hana 'yayan jami'an gwamnati karatu a kasashen waje

Zaben 2019: Hukumar NYSC zata baiwa INEC matasa 20,000 don zama jami'an zabe

Zaben 2019: Hukumar NYSC zata baiwa INEC matasa 20,000 don zama jami'an zabe
Source: Facebook

A cewarsa, INEC ta sannya ranar 14 ga watan Disamba ta zama ranar karshe na turawa da sunayen matasan don yi aiki a zaben, sai su zasu kammala tura sunayen nasu a ranar 6 ga watan Disamba, saboda yin aiki gabanin lokaci.

Momoh ya ce matasan sun samu horo daga INEC kan yadda zaben zai gudana da kuma yadda zasuyi amfani da na'urar tantance masu kada kur'a.

"Ina so in tabbatar maku cewa kwamitin kula da tsaro a zaben, wanda yake karkashin kwamishinan 'yan sanda ya sanya matakai da su tabbatar da kare lafiya da rayukan matasa masu yiwa kasa hidima da zasu yi aikin zaben," a cewarsa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel