Ina da bala'in kudi, kuma ganima ce ba daga gwamnati ba - Pastor Oyedepo

Ina da bala'in kudi, kuma ganima ce ba daga gwamnati ba - Pastor Oyedepo

- Babban Fada na Najeriya, yace bai taba karbar kudi daga hannun ko wace gwamnati ba

- Ina da arziki duk abinda nake so ina samu wannan shi ake kira da dukiya, cewar Bishop

- Ya janyo hankalin 'yan siyasa cewa su fahimci cewa karfin iko yana coci, idan coci tace ba inda zakaje babu wani abu da zaka iyayi akai

Ina da ba;a'in kudi, kuma ganima ce ba daga gwamnati ba - Pastor Oyedepo

Ina da ba;a'in kudi, kuma ganima ce ba daga gwamnati ba - Pastor Oyedepo
Source: Depositphotos

Pastor Dr David Oyedepo, limanin coci mafi girma a kasar nan, yayi kuri da cewa, bai taba karbar dukiya daga gwamnati ba, ko ta yanzu ko ta da can. Ya kuma ce tunda yake bai taba karbar wani abu daga wajen Muhammadu Buhari da ma Goodluck ba.

Yace Ubangiji ya albarkaci albarkaci rayuwarsa; "Ban taba karbar ganima a hannun kowacce gwamnati ba, ina da arziki mai tarin yawa, kuma ina samun duk abinda nake nema wannan shi ake kira da duniya".

Oyedepo ya bayyana haka ne a yayin taron Shiloh na shekara ta 2018 wanda ya hada da manyan limaman coci wanda yake gudana a Ota dake jihar Ogun.

Ana sa rai ya fadi hakan ne bisa ba'a ga Reverend Father Mbaka wanda yayi tsinuwa ga Peter Obi abokin takara na Atiku, wanda qememe yaki biyan sadakarsa a coci, bayan kuma haka aka saba amsar kudaden da sunan Yesu.

DUBA WANNAN: Aikin Oshiomhole ya sake dawowa baya, lokacin da tsohon shugaban APC Oyegun ke neman dawowa kujerarsa

Limamin yayi kira ka .yan siyasa da su fahinci cewa yanzu karfin iko yana coci Wanda idan coci tace ba inda zaka to fa babu abinda zaka iya yi.

Ya fadawa cincirindon mutanen dake wajen wadanda suka hada da jagorori 4,512 daga kasashen duniya 43 cewa a wadannan kwanakin karshe ubangiji zai tabbatar musu da hakan wanda idan coci tana fushi da wani to fa ya gama tabewa.

Taron wanda za'a kareshi da nuna godiya a ranar Lahadi 9 ga watan Disemba shine karo na 20 wanda ake gudanar da addu'o'i da sauran abubuwan ibada

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel