Duk kudin da muka kamo zamu jefa su ayyukan dake cikin kasafin badi - gwamnati

Duk kudin da muka kamo zamu jefa su ayyukan dake cikin kasafin badi - gwamnati

- Za'ayi amfani da kudin hukumar EFCC ta kwace wajen yin ayyukan da gwamnati ta fitar

- Abubakar Malami ne ya bayyana hakan a yayin wani taro daya gudana a jiya

- Gwamnatin ta karbi kudin haraji wanda yawansu yakai miliyan N13.8m

Duk kudin da muka kamo zamu jefa su ayyukan dake cikin kasafin badi - gwamnati

Duk kudin da muka kamo zamu jefa su ayyukan dake cikin kasafin badi - gwamnati
Source: Instagram

Gwamnatin tarayya tace zatayi amfani da duk wani kudi ta hukumomin dake yaki da barayin gwamnati suka tara wajen yin ayyukan data tsara.

Antoni Janar na gwamnati kuma ministan shari'a Abubakar Malami (SAN) shine ya bayyana haka a jiya a yayin wani taro daya gudana a Abuja.

Da yake tofa albarkacin bakin sa a wajen taron mataimakin Shugaban kasa na musamman akan sha'anin kudi Mr. Abiodun Aikomo yace "An bada himma sosai akan kudaden da aka karba don ganin gwamnati tayi amfani dasu akan kudure kuduren ta data gabatar".

DUBA WANNAN: Atiku yace zai tada tattalin arzikin Najeriya idan ya zama Shugaban kas

Ya kara da cewa "A karkashin shirin da akayi na tonawa barayin gwamnati asiri da kuma dakatar da rashawa a kasar,gwamnati ta tara kudi wanda yawan su yakai naira miliyan N13.8m. A watan Mayu gwamnatin ta biya miliyan N439.2m ga wadanda suka tona barayin gwamnati a kalla mutane 14."

Daga 29 ga watan Mayu 2015 zuwa 22 ga watan Nuwamba 2017 gwamnatin ta karbi kudi a hannun ta wanda sukakai miliyan 769.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel