Yanzunnan: Kotu ta sauke shugaban jam'iyyar APC na jihar Anambra

Yanzunnan: Kotu ta sauke shugaban jam'iyyar APC na jihar Anambra

- Wata kotu ta soke zaben Mr Emeka akan matsayin ciyaman na jam'iyar APC

- Wani mamba na jam'iyar ne ya shigar da karar a bisa zaben daya gudana a watan Mayu

- Wanda ya shigar da karar yace shi dan jam'iyar ne na asali sannan shike da burin zama ciyaman na jam'iyar

Yanzunnan: Kotu ta sauke shugaban jam'iyyar APC na jihar Anambra

Yanzunnan: Kotu ta sauke shugaban jam'iyyar APC na jihar Anambra
Source: Depositphotos

A ranar Alhamis ne wata kotu dake zaman ta Awka jihar Anambra ta soke zaben Mr Emeka Ibe a matsayin ciyaman na jam'iyar APC a jihar.

Chief Uzochukwu Onyekwere mamba a jam'iyar ta APC shine ya shigar da karar inda yake kalubalantar zaben da akayi a 19 ga watan Mayu.

Wadanda ake tuhuma akan wannan batu sun hada da Okey Ezea,Rep.Kingsley Chinda,ciyaman na jam'iyar APC a jihar Anambra Ibe wanda ke kurin cewa shine yaci zaben sannan kuma da hukumar zabe ta INEC.

Onyekwere ya bayyana wa kotu cewa shi dan jam'iyar APC ne na asali sannan shi yakamata a bawa kujerar.

Ibeh ya nemi kotu da karta hukuntashi sannan a sanya batun zaben da akayi a 19 ga watan Mayu a gefe.

DUBA WANNAN: Makudan kudaden da aka kwato daga barayin wancan mulkin ar sun fara shiga manyan ayyuka na kasa

Bayan gama saurarar wadanda ake tuhumar na tsayin awanni biyu mai shari'a Bature Gafai ya kure rubutacciyar rantsuwa da wadanda ake tuhumar sukayi inda yace kotu bata da hurumi akan wannan lamari wanda ya kasance batu ne na gida.

Sannan ya soke zaben ciyaman na APC ya bada umarnin a sake wani zaben wanda hukumar INEC zata sanya ido akai.

Onyekwere yace zai koma yayi shiri a bisa zaben da za'a sake wanda hakan shine zai samar da kwanciyar hankali a jam'iyar.

Ya kara da cewa" zanje na shirya idan ni naci wannan zabe zanyi farin ciki idan ma bani bane shima zanyi farin ciki tunda munsan anyi mana adalci".

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel