Gwamnatin tarayya ta gurfanar da Dino Melaye a kan sabuwar tuhuma

Gwamnatin tarayya ta gurfanar da Dino Melaye a kan sabuwar tuhuma

Gwamnatin tarayya a ranar Laraba, 5 ga watan Disamba ta bude sabon shari’a akan Sanata Dino Melaye a gaban babban kotun tarayya da ke babbar irnin tarayya a Maitama, Abuja, inda ake tuhumar shi da bayar da bayanan karya akan shugaban ma’aikata na Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi, Mista Edward Onoja.

Shari’an na tattare da tuhume-tuhume biyu akan Melaye inda ake zarginsa da ba yan sanda bayanan karya da gangan domin batawa Onoja suna cewa yana da hannu a yunkurin kashe shi (Melaye).

Yan sandan sun bayyana cewa sun gano zargin karya da Melaye ke yi yayinda suke bincike a zargin yunkurin kashe shi a garinsa na Ayetoro-Gbede da ke jihar Kogi.

Sanatan a ranar 1 ga watan Maris, 2018 ya ki amsa laifin tuhumar da ofishin atoni janar na kasar ke yi masa a ranar 31 ga watan Janairun 2018.

Gwamnatin tarayya ta gurfanar da Dino Melaye a kan sabuwar tuhuma

Gwamnatin tarayya ta gurfanar da Dino Melaye a kan sabuwar tuhuma
Source: Depositphotos

Melaye na a kotu a ranar Laraba lokacin da Onoja ya zo ya tsaya a wajen mai bayar da shaida.

Ana zargin wanda ake karar da bayar da bayanankarya a watan Afrilun 2017 a wani hiera waya da Mista Mohammed Abubakar, dan marigayi tsohon gwamnan jihar Kogi, Aubakar Audu, tare da kudirin bata sunan Onoja.

Onoja yace da kunnensa ya saurari hiran a shafin Saharareporters, jaridar yanar gizo.

Ya bayyana cewa ya kai rahoton lamarin ga yan sanda bayan ya tuntubi yanuwansa, abokai da kuma lauyoyinsa sannan suka ce ya kai kara ga hukumar yan sanda.

KU KARANTA KUMA: 2019: Karshen mulkin Shugaba Buhari ya karaso - Inji Jam'iyyar PDP

Onoja yace ya kai rahoton lamarin ta wani korafi da ya rubuta ga kwamishinan yan sanda a jihar Kogi.

Justice Olasunbo Goodluck a ranar Laraba ya dage sauraron shari’an zuwa ranar 14 da 28 ga watan Janairu, 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel