Majalisar wakilai ta janye kudurin dokar hana 'yayan jami'an gwamnati karatu a kasashen waje

Majalisar wakilai ta janye kudurin dokar hana 'yayan jami'an gwamnati karatu a kasashen waje

- Majalisar wakilan tarayya ta ki amincewa da kudurin dokar da ke son hana jami'an gwamnati tura 'yayansu karatu a kasashen waje

- Da yake gabatar da kudurin, Sergius Ogun, ya ce manufar dokar shine sa ido kan yadda jami'an gwamnati ke tura 'yayansu karatu a kasashen waje, wanda ke nakasa karatu a Nigeria

- Sai dai da yawa daga cikin 'yan uwansa a majalisar sun bukaci a yi watsi da wannan kudurin doka, kasancewar ya saba da 'yancin da doka ta baiwa kowanne dan Nigeria

Majalisar wakilan tarayya ta ki amincewa da kudurin dokar da ke son hana jami'an gwamnati tura 'yayansu karatu a kasashen waje. Yan majalisar sun tafka muhawara kan cewar sa hannu a dokar zai tauye 'yancin 'yan Nigeria, musamman ma 'yancin tafiye tafiye.

Da yake gabatar da kudurin gaban majalisar a ranar Laraba, Sergius Ogun, daga jihar Edo, ya ce manufar kudurin dokar shine sa ido akan yadda jami'an gwamnati ke tura 'yayansu karatu a kasashen waje, wanda hakan ke nakasa karatu a cikin kasar Nigeria.

Sai dai da yawa daga cikin 'yan ujwansa 'yan majalisar sun bukaci a yi watsi da wannan kudurin doka, kasancewar ya saba da 'yancin da doka ta baiwa kowanne dan Nigeria. Uzoma Abonta daga jihar Abia ya ce akwai makamancin wannan kudurin doka da aka taba tattaunawa akansa, kuma majalisar tayi watsi dashi.

KARANTA WANAN: Karka biyewa masu kokarin hanaka sa hannu a kudurin dokar zabe - Saraki ya shawarci Buhari

Majalisar wakilai ta janye kudurin dokar hana 'yayan jami'an gwamnati karatu a kasashen waje

Majalisar wakilai ta janye kudurin dokar hana 'yayan jami'an gwamnati karatu a kasashen waje
Source: Depositphotos

Femi Gbajabiamila daga jihar Legas shima ya ce kudirn dokar ta sabawa tsarin demokaradiyya "musamman ganin ta tauye 'yancin ra'ayi, tafiye tafiye, rayuwa bisa tsarin mutum da dai sauransu," wanda ya ce babu yadda za a iya gyara karatun kasar ta hanyar hana mutane fita wasu kasashen yin karatu.

Daga karshe, Yakubu Dogara, kakakin majalisar wakilan tarayyar, ya bayar da umurnin a mayar da kudurin dokar zuw1a ga kwamitin dokoki da kasuwanci don yin nazari akansa da kuma duba batun kan 'yancin dan Adam da yake ta'allaka da kudurin dokar.

An janye kudurin dokar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel