Obasanjo na gayyatar fushin Allah - Oshiomhole

Obasanjo na gayyatar fushin Allah - Oshiomhole

Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa Adams Oshiomhole a jiya Laraba, 5 ga watan Disamba ya bayyana cewa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo na gayyatar fushin Allah.

Shugaban na APC ya caccaki tsohon shugaban kasar kan goyon bayan tsohon mataimakinsa, Atiku Abubakar da ke neman kujerar shugaban kasa bayan ya fada ma duniya cewa Allah ba zai yafe masa ba idan ya mara masa baya.

Obasanjo ya lashe amansa bayan shugaban cocin katolika na Sokoto Diocese Matthew Hassan Kukah da wasu malaman addini sun sasanta shugabannin.

Obasanjo na gayyatar fushin Allah - Oshiomhole

Obasanjo na gayyatar fushin Allah - Oshiomhole
Source: UGC

Oshiomhole wanda yayi Magana yayinda ya tarbi shugabannin mata a APC da Edo da babbar birnin tarayya, ya caccaki tsohon shugaban kasar cewa yana gayyatar fushin Allah ta hanyar marawa Atiku baya.

KU KARANTA KUMA: 2019: Oshiomhole yayi kaca-kaca da 'Dan takarar PDP Atiku Abubakar

Jigon APC din ya kuma caccaki Gwamna Rochas Okorocha na jihar Imo da Ibikunle Amosun na Ogun akan karfafa gwiwar magoya bayansu na su koma wata jam’iyyar domin cimma kudirinsu bayan sun fadi zaben fidda gwani.

Dukkanin gwamnonin biyu sun yi alkawarin marawa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari baya amma cewa za su tabbatar da nasarar zabinsu a wasu jam’iyyu.

Oshiomhole ya jadadda cewa APC zata yi nasara koda kuma babu su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel