ASUU ta fadawa Malaman Jami’a su kara daramar dogon yajin aiki

ASUU ta fadawa Malaman Jami’a su kara daramar dogon yajin aiki

- Kungiyar ASUU ta shiga wani yajin aikin da har yau an rasa lokacin da za a kare

- Yanzu haka ‘Dalibai na gida a zaune saboda yajin da Malaman Jami’o’in su ke yi

- ASUU sun ce ba za su janye yajin aikin ba har sai Gwamnati ta cika alkawuran ta

ASUU ta fadawa Malaman Jami’a su kara daramar dogon yajin aiki

Malaman Jami'o'in Gwamnati su na yajin aiki a Najeriya
Source: UGC

Bisa dukkan alamu dai, babu ranar dawowa daga yajin aikin da Malaman Jami’o’in Najeriya na Kungiyar ASUU su ka shiga makonni fiye da 5 da su ka wuce. Yanzu haka dai ASUU ta fadawa ‘Ya ‘yan ta cewa su kara zage dantse.

Shugaban Kungiyar nan ta ASUU na Kasa baki daya, Farfesa Biodun Ogunyemi ya fadawa Malaman Jami’o’i cewa su kara azamar shiryawa dogon yajin aikin da babu ranar dawowa, Har yanzu dai ‘Daliban kasar su na gida.

KU KARANTA: Makauniyar da ta kammala karatun shari’a ta gana da Gwamnan Kaduna

Ogunyemi yace hakan ya zama dole ne a sakamakon rashin cika alkawarin da Gwamnati ta dauka na gyara harkar ilmi a fadin kasar. Kungiyar ASUU tana ikirarin Gwamnatin Najeriya ba ta narkar kudin da su ka dace a harkar ilmi,

A wata takarda da Shugaban ASUU ya fitar a kwanan baya, yayi kira ga ‘Ya ‘Yan Kungiyar da su sake zage dantse, su kuma kauda kai daga duk wata barazana da Gwamantin Tarayya za tayi wa Malaman Makarantar game da yajin.

Yanzu dai tattaunawar Gwamnatin da Malaman na Jami’o’i ya gaza haihuwar ‘da mai ido. Shugaban Kungiyar ASUU na Jami’ar Ibadan, Dr Deji Omole ya nemi hadin kan Jama’a inda yayi kira ga Iyaye su guji biyewa zugar ‘Yan siyasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel