Ku kadawa shugaba Buhari kuri'un ku a Zaben 2019 - Gwamna Akeredolu ga masu ribatar shirin N-Power

Ku kadawa shugaba Buhari kuri'un ku a Zaben 2019 - Gwamna Akeredolu ga masu ribatar shirin N-Power

Gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu, ya nemi masu ribatar shirin N-Power da ke fadin kasar nan, akan ramawa Kura kykkyawar aniyyarta ta hanyar kadawa shugaban kasa Muhammadu Buhari kuri'un su yayin babban zabe na 2019.

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito, Gwamna Akeredolu ya nemi masu ribatar shirin na N-Power karkashin gwamnatin shugaban kasa Buhari da mataimakin sa, Farfesa Yemi Osinbajo, akan tabbatar da jefa ma su kuri'u a babban zaben kasa na badi.

Gwamnan ya yi wannan kira ne a babban birnin Akure yayin ganawa da masu ribatar shirin na jihar sa, inda ya ce hakan zai tabbatar da ci gaba na kwararar wannan kyakkyawan tagomashi zuwa ga wasunsu domin ingantawa rayuwarsu da kuma tattalin arziki.

Gwamnan jihar Ondo; Oluwarotimi Akeredolu

Gwamnan jihar Ondo; Oluwarotimi Akeredolu
Source: Depositphotos

A yayin ci gaba da gabatar da jawabansa, Gwamna Akeredolu ya kuma bayyana cewa, shirin N-Power ya bai wa Matasa da dama da ke fadin kasar wata hanya da inganta rayuwarsu gami da bude kofa ta baje kaifin basirarsu da kuma kwazo.

KARANTA KUMA: Majalisar Wakilai ta nemi Buhari ya aiwatar da yarjejeniyar ASUU

Ya kara da cewa, shugaban kasa tare da Mataimakinsa sun cika alkawurran su akan Matasa inda ya yi kira na kwarara ma su yabo da kuma jinjina maras yankewa.

Kazalika jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya sha alwashin inganta rayuwar Matasan kasar nan muddin ya cimma nasara yayin babban zabe na 2019.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel