2019: Oshiomhole yayi kaca-kaca da 'Dan takarar PDP Atiku Abubakar

2019: Oshiomhole yayi kaca-kaca da 'Dan takarar PDP Atiku Abubakar

Mun samu labari cewa Shugaban Jam’iyyar APC mai mulki, Adams Oshiomhole ya dura kan ‘Dan takarar Shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar da kuma tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo.

2019: Oshiomhole yayi kaca-kaca da 'Dan takarar PDP Atiku Abubakar

Shugaban APC yace Buhari zai ba Atiku da Obasanjo kunya
Source: Depositphotos

Kwamared Adams Oshiomhole ya soki Cif Olusegun Obasanjo ne a dalilin goyon bayan ‘Dan takarar PDP kuma tsohon Mataimakin sa watau Atiku Abubakar. Oshiomhole yace dukkan sun dai za su sha kashi ne a zaben 2019.

Oshiomhole yayi kaca-kaca da Atiku Abubakar da kuma Uche Secondus wanda shi ne Shugaban Jam’iyyar PDP a Najeriya bayan sun nemi Sufeta Janar na ‘Yan Sanda da kuma Shugaban Hukumar INEC su yi murabus.

KU KARANTA: Atiku yace zai yi irin abin da Jonathan yayi wajen inganta tattalin Najeriya

Adams Oshiomhole yace Jam’iyyar PDP ta shirya aikata mugun magudi ne a zaben 2019 don haka ta ke neman IGP Ibrahim Idris da kuma Shugaban Hukumar zabe watau Farfesa Mahmood Yakubu su sauka daga mukaman na su.

Shugaban Jam’iyyar mai mulki na kasa watau Oshiomhole yayi wannan bayani ne a lokacin da ya gana da wasu Matan Jam’iyyar da ke Jihar Edo. Matan na APC sun kai wa Oshiomhole ziyarar ban-girma ne har gida a jiya Laraba.

A karshe dai Shugaban na APC ya caccaki wasu Gwamnonin Jam’iyyar da ke kokarin shiryawa APC zagon-kasa. Kwamared Adams Oshiomhole yace za a hukunta Gwamnonin, sannan kuma za su sha kashi a zaben da zai gabata.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel