Yan bindiga sun kutsa kai cikin makaranta, sun sace Malamai 5, sun kashe 1

Yan bindiga sun kutsa kai cikin makaranta, sun sace Malamai 5, sun kashe 1

Wasu gungun yan bindiga sun kai ma wata makarantar gaba da sakandari, kwalejin kimiyya ta jahar Osun dake garin Esa-Oke, farmaki a ranar Talata 4 ga watan Disamba inda suka sace malamai biyar tare da kashe wani jami’in kwalejin.

Majiyar Legit.com ta ruwaito sunan ma’aikacin kwalejin da yan bindigan suka kashe Olaniyi Temitope, inda rahotanni suka tabbatar da cewar yan bindigan sun kashe shine a wani harin mai kan uwa da wabi da suka yi a makarantar.

KU KARANTA: An kama mai kamawa: EFCC ta kama shugaban kungiyar lauyoyin Najeriya da zambar naira biliyan 1.4

Daga bisani kuma yan bindigan sun yi awon gaba da malamin ilimin tafiyar da kasuwanci Olaleye Olalekan, shugaban sashin ilimin kimiyyar gine gine Adeyeoluwa Bankole da sakatarensa, daraktan zuba jarin kwalejin Jesuola Ajibola, sai kuma ma’aikaci a bankin kwalejin Rachael Onyinocha.

Wani malamin makaranta daya bukaci a sakaya sunansa ya shaida ma majiyarmu cewa yan bindigan sun halaka wani jami’in Dansanda da yayi kokarin ceto mutanen biyar, inda bayan nan suka yi awon gaba da shi.

Sai dai a jawabinsa, Kaakakin kwalejin kimiyyar jahar Osun, Adewale Oyekanmi ya bayyana cewa “Yan bindiga sun kai hari akan babban hanyar Esa-Oke da yammacin Talata bayan an tashi aiki, sun yi garkuwa da wasu ma’aikatan kwalejin.”

Amma fa majiyarmu ta kara da cewa zuwa yanzu yan bindigan sun fara tuntubar iyalan wadanda suka yi garkuwa dasu suna neman a biyasu kudaden fansa, sai dai kwamishinan Yansandan jahar Fimihan Adeoye ya bayyana cewa jami’ansa suna bin sawun barayin don tabbatar da ganin sun kamasu.

A wani labarin kuma, an yi garkuwa da wasu ma’aikatan cibiyar kiwon lafiya ta gwamnatin tarayya dake Owo ta jahar Ondo su uku a ranar Laraba 5 ga watan Disamba yayin da suke kan hanyarsu ta komawa gida.

Wadanda aka sace sun hada da wani likitan asibitin, jami’ar jinya da wani jami’in adana bayanan marasa lafiya, kuma an sacesu ne akan hanyarsu ta zuwa garin Owo daga babban birnin jahar Ondo, Akure, a yanzu haka barayin sun nemi a biyasu kudin fansa naira miliyan hamsin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel