Yadda Kotu ta hukunta wani Malami da ya yi ma dalibarsa fyade a makaranta

Yadda Kotu ta hukunta wani Malami da ya yi ma dalibarsa fyade a makaranta

Wata kotun majistri dake zamanta a garin Okitipupa na karamar hukumar Okitipupa ta jahar Ondo ta bada umarnin a garkame mata wani malamin makaranta, Ebenezer Adeyeye a gidan Yari bayan sauraron karar tuhumar da ake yi masa na fyade.

Majiyar Legit.com ta ruwaito ana Yansanda na tuhumar Adeyeye da laifin yi ma wata dalibarsa mai shekaru biyar fyade ne a cikin bayin makarantar firamarin da yake koyawar dake cikin garin Okitipupa a ranar 7 ga watan Nuwamba.

KU KARANTA: An kama mai kamawa: EFCC ta kama shugaban kungiyar lauyoyin Najeriya da zambar naira biliyan 1.4

Rahoton Yansanda ya bayyana cewa Malamin ya yi amfani ne da dabaru daban daban wajen shigar da karamar yarinyar cikin bayin, daga nan ne ya samu damar danneta tare da yi mata fyade, da wannan ne yansandan suke tuhumarsa akan aikata laifin fyade.

Dansanda mai shigar da kara, Ayodeji Omoyegha ya bayyana ma kotun cewa iyayen dalibar ne suka kai karar malamin da suke zargin ya yi ma diyarsu fyade ga ofishin Yansanda, inda Yansanda basu yi wata wata ba suka shiga farautarsa har suka kamo shi.

Bugu da kari Dansandan ya tabbatar ma kotu cewa laifin da ake tuhumar Malamin ya saba ma sashi na 358 na kundin hukunta manyan laifuka na shekarar 2006 na jahar Ondo, don haka ya nemi kotu ta hukunta malamin kamar yadda doka ta tanadar.

Sai dai Malam Adeyeye ya musanta tuhumar yi ma dalibarsa fyade, daga nan ne kuma bayan sauraron dukkanin bangarorin biyu sai Alkalin kotun mai sharia O. Ogunfuyi ya nemi a garkame masa Malamin a kurkuku har sai ya samu umarnin daraktan shigar da kararraki na jahar.

Daga karshe Alkali mai sharia O. Ogunfuyi ya dage sauraron karar zuwa ranar 30 ga watan Janairu na shekarar 2019.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel