Majalisar Wakilai ta nemi Buhari ya aiwatar da yarjejeniyar ASUU

Majalisar Wakilai ta nemi Buhari ya aiwatar da yarjejeniyar ASUU

Da sanadin shafin jaridar The Nation mun samu cewa, Majalisar wakilai yayin gudanar da zamanta ta cimma matsaya tare da yanke shawarar shiga cikin lamarin yajin aiki na malaman jami'o'in kasar nan da ke karkashin kungiyar ASUU.

Mambobin majalisar sun bayyana damuwarsu kwarai da aniyya dangane da yadda yajin aikin kungiyar ASUU ya dakile harkokin karantu a jami'o'in kasar nan a sakamakon yadda gwamnatin tarayya ta gaza aiwartar da yarjejeniyar da ta kulla tare da kungiyar.

Kazalika majalisar ta bayyana rashin gamsuwarta dangane da yadda fadar shugaban kasa ta gaza tare da kekashewa wajen aiwatar da yarjejeniyar ta da kulla da majalisar dokoki ta tarayya kan harkokin da suka shafi sabon mafi karancin albashin ma'aikata na kasar nan.

Majalisar Wakilai ta nemi Buhari ya aiwatar da yarjejeniyar ASUU

Majalisar Wakilai ta nemi Buhari ya aiwatar da yarjejeniyar ASUU
Source: Depositphotos

A sanadiyar wannan lamari ya sanya majalisar ta kafa sabon kwamiti domin aiwatar da bincike gami da dalilai da suka haddasa yajin aiki na mambobin kungiyar ma'aikatan majalisar dokoki ta tarayya da ta afka a ranar Talatar da ta gabata.

KARANTA KUMA: Uwargidan Shugaba Buhari ta barrantar da kanta daga zargin rashawa

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, tabbatar da hukuncin wannan shawara da majalisar ta yanke yayin zamanta ta biyo bayan furucin dan majalisar mai wakilcin jihar Jigawa, Sani Zoro na jam'iyyar APC.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, a yammancin jiya na Laraba, shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya dawo daga tafiyarsa ta halartar taron majalisar dinkin duniya kan sauyin yanayi da aka gudanar a birnin Katowice na kasar Poland.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel