An kama mai kamawa: EFCC ta kama shugaban kungiyar lauyoyin Najeriya da zambar naira biliyan 1.4

An kama mai kamawa: EFCC ta kama shugaban kungiyar lauyoyin Najeriya da zambar naira biliyan 1.4

Hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta cafke wani babban lauya, kuma shugaban kungiyar lauyoyin Najeriya, NBA, Mista Paul Usoro mai lambar girma ta SAN, da laifin satar kudi naira biliyan daya da miliyan dari hudu.

Majiyar Legit.com ta ruwaito a ranar Laraba 5 ga watan Disamba ne EFCC ta shigar da karar shugaban NBA gaban wata babbar kotun tarayya dake jahar Legas kamar yadda takardar shigar da kara mai lamba FHC/418c/18 ya bayyana.

KU KARANTA: Da dumi dumi: Gungun masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da ma’aikata 8

An kama mai kamawa: EFCC ta kama shugaban kungiyar lauyoyin Najeriya da zambar naira biliyan 1.4

Paul Usoro
Source: UGC

Ana sa ran alkalin kotun, mai sharia Muslim Hassan zai sanya ranar da zai fara sauraron karar. Lauyan hukumar EFCC, Rotimi Oyedepo wanda ya rattafa hannu akan takardar shigar da karar ya bayyana cewa laifin da shugaban lauyoyin Najeriya ya tafka ya saba ma sashi na 18 (a) na kundin dokokin hukunta satar kudi na shekarar 2011.

A cewar lauyan EFCC Rotimi, suna sa ran kotu ta hukunta Mista Paul Usoro kamar yadda sashi na 15 (3) ya tanadar domin hakan ya zama izina ga sauran jama’a, musamman masu rike da madafan iko ta yadda zasu zamo masu gaskiya.

Sai dai wani abin mamakin shine ta yadda hannayen shugaban lauyoyin Najeriya gaba daya ya tsomu dumu dumu a cikin badakalar wawuran kudade, mutumin da ake ganin sune masu tsawatarwa game da sata, zamba ko almundahana.

A wani labarin kuma wasu gungun yan bindiga sun yi awon gaba da wasu ma’aikatan kwalejin kimiyya na da jahar Osun dake garin Esa-Oke a ranar Talata 4 ga watan Disamba kamar yadda rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN, ta bayyana.

Kaakakin kwalejin, Adewale Oyekanmi ne ya sanar da haka cikin hirar da tayi da shi a garin Osogbo, inda yace baya gas ace ma’aikatan su takwas, yan bindigan sun halaka wani daga cikinsu dake kokarin tserewa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel