Rikicin siyasa: Yan bindiga sun kai ma dan takarar gwamna hari, sun bindige mutum 2

Rikicin siyasa: Yan bindiga sun kai ma dan takarar gwamna hari, sun bindige mutum 2

Wani babban dan siyasa kuma dan takarar gwamnan jahar Ogun a karkashin jam’iyyar Afarican Democratic Alliance-ADC, Gboyega Nasir Isiaka ya tsallake rijiya da baya bayan wasu yan bindiga sun bude ma ayarin motocinsa wuta.

Majiyar Legit.com ta ruwaito lamarin ya faru ne a unguwar Ibese dake cikin karamar hukumar Yewa ta Arewa inda yan bindigan suka bude ma ayarin motocinsa wuta, suka bindige mutane biyu wadanda a yanzu haka suna cikin halin rai fakwai mutu fakwai.

KU KARANTA: Da dumi dumi: Gungun masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da ma’aikata 8

Kaakakin yakin neman zaben Gboyega, Alhaji Adeniji ne ya sanar da haka a ranar Laraba, inda yace a daidai mahadar hanyar Ibese ne yan bindigan suka yi ma motocinsu kwantan bauna a yayin da suka fito yakin neman zabe.

Adeniji yace duk da cewa jami’an tsaron dake tare dasu a cikin ayarin motocin sun mayar da wuta akan yan bindigan, inda suka rakasu har cikin daji, amma duk da haka sai da suka bude wuta irin na mai kan uwa da wabi, inda suka jikkata mutane biyu.

Sai dai kaakakin ya bayyana harin a matsayin wata makarkashiya, don haka yayi kira ga jami’an tsaron dake jahar dasu kaddamar da bincike domin su tabbata sun kama yan bindigan da duk wadanda keda hannu cikin harin.

“Mun yi mamakin yadda aka kawo mana hari kwana daya bayan ganawar babban sufetan Yansandan Najeriya da jam’iyyun siyasa inda aka tattauna hanyoyin samar da zaman lafiya a yayin zaben 2019 da bayansa, don haka muna kira a kara yawan jami’an tsaron dake gadin Maigidanmu.” Inji shi.

Sai dai da majiyarmu ta tuntubi kaakakin rundunar Yansandan jahar, Abimbola Oyeyemi don jin ta bakinsa game da harin, sai yace babu wanda ya kawo musu rahoto har zuwa lokacin tattara rahotonnan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel