Zan babbako da tattalin kasar nan idan aka zabe ni – Atiku Abubakar

Zan babbako da tattalin kasar nan idan aka zabe ni – Atiku Abubakar

Mun samu labari jiya Laraba cewa ‘Dan takarar PDP na Shugaban kasa, Atiku Abubakar yayi alkawarin gyara tattalin Najeriya idan ya samu mulkin kasar nan a babban zaben da za ayi shekara mai zuwa.

Zan babbako da tattalin kasar nan idan aka zabe ni – Atiku Abubakar

Atiku Abubakar yayi alkawarin gyara tattalin arzikin Najeriya
Source: Depositphotos

Alhaji Atiku Abubakar yayi wannan alkawari ne a wajen yakin neman zaben Jam’iyyar PDP. Jam’iyyar hamayyar ta shirya wani gangami na musamman domin Yankin Arewa maso tsakiyar Najeriya ne a Ranar Larabar nan.

Atiku ya bayyana cewa zai yi irin abin da tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan yayi a lokacin mulkin sa inda Najeriya ta zama Kasar da ta fi kowace karfin tattalin arziki a kaf Nahiyar Afrika daga 2011 zuwa shekarar 2015.

KU KARANTA: Wani Malami ya debo ruwan dafa kan sa bayan ya caccaki ‘Dan takarar PDP

‘Dan takarar Shugaban kasar ya kuma sha alwashin kawo karshen tashin-tashinar da ake yi a Yankin Arewa maso Gabashin Kasar nan. Atiku yayi wannan jawabi ne duk a Garin Ilorin a cikin Jihar Kwara wajen yawon kamfe.

Wazirin na Adamawa, Atiku Abubakar yayi kira ga Mutanen Jihar Kwara da sauran al’ummar Yankunan na tsakiyar Arewacin Najeriya da su mara masa baya a zaben 2019 domin ganin ya tika Jam'iyyar APC mai mulki da kasa.

Sauran Jiga-jigan Jam’iyyar ta PDP sun halarci wannan taro da aka shirya inda Shugaban PDP na kasa, Prince Uche Secondus yayi kira ga Jama’a a zabi PDP a shekara mai zuwa domin ceto al’ummar Kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel