Aikin gwamna na da wahala, ji nake tamkar na tsere - El-Rufa'i

Aikin gwamna na da wahala, ji nake tamkar na tsere - El-Rufa'i

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya ce ko shakka babu abu ne mai matukar wahala jagorancin al'umma masu yawa.

A jawabin da ya yi wajen taron zaben da lafiya da Kaduna State Peace Commission ta shirya, gwamnan ya ce sau da yawa yakan ji kamar ya tattara ya gudu ya bar mulkin kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Ya ce bai zai yi jayaya ba muddin ya fadi zaben takarar gwamna na shekarar 2019, inda ya kara da cewa zai kwashe komatsensa cikin hanzari ya fice daga gidan gwamnatin.

Gwamnan ya ce burin jam'iyyar All Progressives Congress APC shine ta ganin ta gudanar da babban zaben cikin zaman lafiya.

DUBA WANNAN: Ku rage albashinku, ya yi yawa gaskiya - Babban Sarki ya fadawa sanatocin Najeriya

Aikin gwamna na da wahala, ji nake tamkar na tsere - El-Rufa'i

Aikin gwamna na da wahala, ji nake tamkar na tsere - El-Rufa'i
Source: Depositphotos

"Zan fara tsokaci a matsayina na dan takarar gwamna na APC, burin jam'iyyar mu shine gudanar da zabe cikin zaman lafiya. Jam'iyyun da suka hade suka kafa APC sun gamu da magudin zabe da rikicin da ya faru bayan zabe," inji shi.

"Magudin zabe ne ke haifar da rikici. Tsantsagwaron magudin zaben da aka tafka a 2011 ne ya janyo rikice-rikice a wannan lokacin inda a jihar Kaduna kawai mutane sama da 800 ne suka rasa rayyukansu.

"A matsayina na dan takarar APC, Ina fada muku zan kwashe kayayakina cikin hanzari in fice daga gidan gwamntai idan al'umma ba su zabe ni ba.

"Ni ne zan fara amincewa da kayen kuma ina son in fada wa wadanda ke son zama gwamna su sani cewa aikin yana da matukar wahala ... Ina son in gudu.

"Kawai dai idan na kali wadanda ke son zama gwamna da irin abubuwan da suka aikata a baya a jihar, sai in ga cewa akwai bukatar in kare jihar da al'ummar jihar daga miyagun ayyukan da wadanda suka aikata a baya." inji El-Rufai.

Gwamnan kuma ya yi alkawarin hukunta duk wani da aka samu yana yada kalaman kiyaya ko kawo rikicin addini a kafafen sada zumunta a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel