Ministan kwadago ya karbi ragamar tattaunawa da ASUU

Ministan kwadago ya karbi ragamar tattaunawa da ASUU

Ministan kwadago da samar da aiyuka na kasa, Dakta Chris Ngige, ya karbi ragamar cigaba da tattaunawa da kungiyar malaman jami'oi ta kasa dake yajin aiki. Ministan ya karbi aikin cigaba da yunkurin kawo sulhu tsakanin ASUU da gwamnatin tarayya.

Domin kaucewa samun tangarda da gaggauta kawo karshen dukkan wani sabani, ministan kwadago, Sanata Chris Ngige, zai karbi ragamar cigaba da tattaunawa tsakanin malaman jami'o'in Najeriya dake yajin aiki da kuma gwamnatin tarayya.

A wani jawabi da aka rabawa manema labarai, Ngige ya yi Alla-Wadai da da kalaman babban lauyan Najeriya, Femi Falana (SAN), a kan cewar yin amfani da sashe na 43.1 na tsarin dokokin ma'aikata na kin biyansu albashi yayin da suka shiga yajin aiki ya saba doka.

Falana ya bayyana cewar dokar kin biyan ma'aikata albashi saboda sun shiga yajin aiki haramtaciyya ce tare da umartar gwamnatin tarayya ta gaggauta janye kudirinta na yin amfani da dokar a kan malaman jami'o'in Najeriya dake yajin aiki.

Ministan kwadago ya karbi ragamar tattaunawa da ASUU

Chris Ngige
Source: Depositphotos

Ministan ilimi, Adamu Adamu, ne ke jagorantar zaman sulhu da gwamnatin tarayya tun bayan fara yajin aikin ASUU, sai dai yanzu, Ngige ya ce ya karbi ragamar cigaba da tattaunawar bisa dogaro da ikon da sashe na 5 na kundin tsarin sulhu da ma'aikata ya bawa ofishin ministan kwadago.

Da wannan sabon tsari ne, Ngige, ya yi amfani wajen aike takardar gayyatar zama na musamman ga shugabannin kungiyar ASUU da masu ruwa da tsaki a dakin taro na ma'aikatar kwadago, ranar Litinin mai zuwa.

DUBA WANNAN: Abinda yake firgita APC dangane da zaben 2019 - Ghali Na'abba

Tun farkon watan Nuwamba ne kungiyar malaman jami'o'i ta sanar da shiga yajin aikin sai baba-ta-gani bisa dalilan cewar gwamnatin tarayya bata warewa bangaren ilimi isassun kudade domin gudanar da aikin koyo da koyarwa a jami'o'in kasar nan.

Kazalika, malaman sun zargi gwamnatun tarayya da gaza cika alkawarin da ta daukar ma su na bayar da kudaden gudanarwa ga jami'o'i kamar yadda suka cimma yarjejeniya a baya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel