Gwamna Bello ya tsige Kwamishina, ya yi sabbin nade-nade 16

Gwamna Bello ya tsige Kwamishina, ya yi sabbin nade-nade 16

Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi tsige kwamishinan Al'adu da yawon bude idanu na jihar daga Mr Arome daga mukaminsa kuma ya amince da nadin sabbin hadimansa guda 16.

Sanarwar da ta fito daga bakin sakataren gwamnatin jihar, Mrs Folashade Ayoade a ranar Laraba ta tabbatar da murabus din Adoji amma ba ta bayyana dalilan tsige shi ba.

Ayoade ya ce gwamnan ya zabi Dr Paul Ugbede Ebije domin ya maye gurbin kwamishinan da aka kora.

Gwamna Bello ya tsige Kwamishina, ya yi sabbin nade-nade 16

Gwamna Bello ya tsige Kwamishina, ya yi sabbin nade-nade 16
Source: Twitter

Sanarwar ta kuma ce an nada Mr Aliyu Salami a matsayin sabon shugaban hukumar tattara kudaden shiga na jihar ta Kogi.

DUBA WANNAN: Albashi ne zai nuna alkiblar ma'aikata a zaben 2019 - Kungiyar Kwadago

Salami ya maye gurbin Alhaji Yakubu Oseni, wadda a yanzu shine dan takarar kujerar Sanata na jam'iyyar APC a mazabar Kogi ta tsakiya a zaben 2019.

Sauran mutanen da aka yiwa nadi sun hada da Mr Umar Abdulshi da Mr Mudi Yusuf a matsayin mambobin hukumar gudanarwa na kananan hukumomin Lokoja da Ofu.

Sauran wadanda aka yiwa nadin sun hada da Mr Suleiman Abubakar, Mr Segun Aberepran, Mr Yahaya Halilu, Mr Mathew Malik, Mr Abubakar Abdulkarim a matsayin manyan masu taimakawa gwamna na musamman yayin da Mr Salihu Idachaba, Hajia Halimatu Amodu da Mr Nda Aron an nada su a matsayin mataimakan gwamnan na musamman.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel