Babu wani shiri na hana mutane amfani da kafafen sada zumunta - Ministan Sadarwa

Babu wani shiri na hana mutane amfani da kafafen sada zumunta - Ministan Sadarwa

Gwamnatin tarayya ta tabbatar wa 'yan Najeriya cewa babu wani shiri da hukumomin ta keyi domin hana 'yan Najeriya amfani da kafafen sada zumunta kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ministan sadarwa, Adebayo Shittu ne ya bayar da wannan sanarwan a jiya Laraba a yayin da ya ke jawabi ga mahalarta taron kasa na kafafen sada zumunta mai taken "Amfani da kafar sada zumunta domin inganta mulki".

Ya ce 'yan Najeriya suna da damar su cigaba da tattauna a kan tsare-tsaren gwamnati da tafka muhawarra na siyasa da tona asirin masu rashawa da bayyana ra'ayoyinsu ta kafafen sada zumunta ba tare da amfani da kalamen batanci ko kiyaya ba.

Babu wani shirin saka takunkumi game da amfani da kafafen sada zumunta - Minista

Babu wani shirin saka takunkumi game da amfani da kafafen sada zumunta - Minista
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Ku rage albashinku, ya yi yawa gaskiya - Babban Sarki ya fadawa sanatocin Najeriya

Ministan ya yi kira ga wadanda ke amfani da kafafen sada zumunta su kiyaye kansu daga shagala da ke tattare da kafafen sada zumunta, su mayar da hankulansu zuwa abubuwa masu amfani.

Shittu ya yi bayani cewa barin kowa ya tofa albarkacin bakinsa a kafafen sada zumunta alama ce da ke nuna gwamnatin tarayya tana mutunta ka'idojin demukradiyya.

Ya kuma ce gwamnatin tarayya za ta fara amfani da kafafen sada zumunta wajen gudanar da wasu ayyukanta da kuma tabbatar da nasarar wasu shirye-shiryen gwamnati da za su amfani al'umma.

A jawabin ta, Famanan sakatare na ma'aikatar sadarwa, Mrs Nkechi Ejele ta ce gwamnatin tarayya ta gano amfanin kafafen sada zumunta da yadda ake amfani da su wajen ilimantar da al'umma a kan tsare-tsaren gwamnati.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel