Mutum 60m ne basu da ilimin Boko a Najeriya, inji Adamu Adamu

Mutum 60m ne basu da ilimin Boko a Najeriya, inji Adamu Adamu

- Najeriya na da kusan matasa miliyan 60 da basu iya rubutu da karatu ba

- Mata ne suka kwashe kashi sittin na matasan da basu iya rubutu da karatu

- Yara miliyan 11 ne basa zuwa makaranta

Mutum 60m ne basu da ilimin Boko a Najeriya, inji Adamu Adamu

Mutum 60m ne basu da ilimin Boko a Najeriya, inji Adamu Adamu
Source: UGC

Ministan ilimi, Malam Adamu Adamu, a kano yace matasan Najeriya kusan miliyan 60 ne basu iya rubutu da karatu ba.

Adamu ya wakilci Mista Prinzo James, mataimakin daraktan Basic and secondary Education, ma'aikatar ilimi, ya sanar da hakan a murnar zagayowar ranar rubutu da karatu ta duniya ta shekarar 2018.

Yace mata ne suka kwashe kashi sittin na jimillar wadanda basu iya rubutu da karatu ba, inda yaran da basu zuwa makaranta sun kai miliyan 11.

Kamar yanda ya fada, rashin sana'ar hannu ga wadanda suka kammala karatu ya na kara dagula al'amarin.

Adamu yace halin da kasar ke ciki na bukatar matakin gaggawa.

DUBA WANNAN: Kiwon laifya yayi wa manya katutu, maiqo, taiba, kitse, da kin motsa jiki, da ma shaye-shaye sun zama annoba

"Da wannan kiyasin dake hannun mu, ya zamo shaida kenan akan bukatar gaggauta kawo karshen rashin iya rubutu da karatu tsakanin matasa, yara da kuma manya a kasar nan. Don haka duk wani yunkuri na jawo hankalin masu ruwa da tsaki don kawo karshen matsalar nan zai samu goyon baya daga ma'aikatar ilimi." inji Adamu

"Inaso in tabbatar muku cewa Gwamnatin tarayya na shirye shiryen kaddamar da gagarumin yaki da rashin iya rubutu da karatu a kasar nan," inji shi.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel