Abinda yake firgita APC dangane da zaben 2019 - Ghali Na'abba

Abinda yake firgita APC dangane da zaben 2019 - Ghali Na'abba

Tsohon shugaban majalisar wakilai, Ghali Umar Na'abba, ya yi wata hira da jaridar Guardian inda ya yi maganganu masu yawa a kan harkokin siyasa, musamman batutuwan da suka shafi aiyukan majalisa a karkashin gwamnatin APC.

Da yake amsa tambaya a kan yadda yake ganin yiwuwar karbar mulki daga hannun jam'iyyar APC a shekarar 2019, Na'abba ya ce tabbas baya tsammanin jam'iyyar APC zata bari mulki ya bar hannunta saboda tsoron halin da zata tsinci kanta a hannun jam'iyyar PDP da muzgunawa bayan ta karbi gwamnati a hannunta.

"Bana son a ce nayi mugun baki. Amma, abinda nayi imani da shi shine wannan gwamnatin, bisa la'akari da yadda ta muzgunawa ta mambobin jam'iyyar PDP, ba zata yarda ta bar mulki ba.

"Wannnan na daga cikin rudanin gwamnati, ka ci mutuncin abokan hamayyar ka amma kana tsoron ya yi maka irin abinda ka yi masa.

Abinda yake firgita APC dangane da zaben 2019 - Ghali Na'abba

Ghali Umar Na'abba
Source: Facebook

"Irin wannnan yanayin ne ya saka firgici a zukatan mahukuntan wannan gwamnatin. Haka ne yasa koda yaushe nake shawartar jama'a kan cewar 'kar ka yiwa mutum abinda baka son a yi maka'," a kalaman Na'abba.

Da yake amsa tambaya a kan zargin gwamnatin APC kan cewar PDP ce ta lalata komai a Najeriya, Na'abba ya ce akwai alamun yaudara a wannan zargi.

DUBA WANNAN: Atiku ya fadi dalilin da yasa aka kulle mahaifinsa a gidan yari

"Ina so ku yiwa wannan zargi duba na tsanaki. Muna da tsarin gwamnati a matakin tarayya da jihohi. Tabbas jam'iyyar PDP ta shafe shekaru 16 tana mulki a Najeriya, amma hakan ba yana nufin ta kwashe wa'adin tsawon wadannan shekaru tana mulki a dukkan jihohin Najeriya ba. Jam'iyyu irinsu AD, AC, ACN, APP, ANPP, CPC, APGA, APC da sauransu sun yu mulki a jihohi daban-daban amma babu cigaba a jihohinsu.

"Maganar tabarbarewar gwamnati bai tsaya iya kan gwamnatin tarayya ba kadai, har da jihohin da PDP ba ta taba mulkar su ba, saboda haka ba za a zarge ta ita kadai ba," a cewar Na'abba

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel