Oshiomhole na da mugun nufi a kan APC - Rochas

Oshiomhole na da mugun nufi a kan APC - Rochas

- Ana cigaba da musayar maganganu tsakanin gwamna Imo Rochas Okorocha da Ciyaman din APC na kasa Adams Oshiomhole

- Rikicin na su ya sama asali ne sakamakon hana Okorocha zabin dan takararar gwamnan da zai gaje shi da Oshiomhole ya ki amincewa da hakan

- Gwamna Rochas ya ce Oshiomhole mugun nufi ya shigo da ita APC kuma idan ba ayi taka tsan-tsan ba zai ruguza jam'iyyar

Oshiomhole na da mugun nufi a kan APC - Rochas

Oshiomhole na da mugun nufi a kan APC - Rochas
Source: Facebook

Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha ya yi kaca-kaca shugaban jam'iyyar APC na kasa Adams Oshiomhole inda ya ce inda ya ce Oshiomhole ya zama alakaikai ga jam'iyyar kuma yana gab da ruguza jam'iyyar.

Okorocha ya mayar da martani ne kan kalaman da aka ce Oshiomhole ya fadi a kansa da takwaransa na jihar Ogun, Ibikunle Amosun inda ya ce sun zama matsala ga APC kuma basu da wata kuri'a da ta wuce guda.

DUBA WANNAN: Albashi ne zai nuna alkiblar ma'aikata a zaben 2019 - Kungiyar Kwadago

Okorocha ya ce shugaban jam'iyyar yana girbar abubuwan da ya shuka ne.

A sanarwar da Okorocha ya bayar ta bakin kwamishinan yada labarai na jiharsa, Patrick Nzeh, ya ce APC ta rasa magoya baya kimanin miliyan 10 tun bayan da Oshiomhole ya zama shugaban jam'iyyar.

Ya kuma ce dan takarar gwamna na jam'iyyar Action Alliance, Uche Nwosu zai kayar da dan takarar gwamnan jihar APC a jihar Imo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel