Uwargidan Shugaba Buhari ta barrantar da kanta daga zargin rashawa

Uwargidan Shugaba Buhari ta barrantar da kanta daga zargin rashawa

Mun samu rahoton cewa, Uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha Buhari, a yau Laraba ta barrantar da kanta daga zargin rashawa da a halin hukumar 'yan sandan fararen kaya ta DSS ke gudanar da bincike.

Cikin wata sanarwar da kakakin uwargidan shugaban kasar ya gabatar, Haruna Suleiman ya bayyana cewa, Hajiya Aisha ko kadan ba ta da wata alaka ta kusa ko ta nesa dangane da gudanar da harkokin kasuwanci a Ofishinta da ke fadar shugaban kasa ta Villa a babban birnin kasar nan na tarayya.

A sanadiyar haka Uwargidan ta shugaban kasa ta bayyana cewa, ko kadan ba ta da wata alaka ta aiwatar da duk wasu harkokin samun abin duniya a ofishinta kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito.

Ta kuma yi gargadi ga masu kulla duk wata alakar samun kudi da ma'aikatan ofishinta, inda ta ce kada su kuka da kowa face kawunan su yayin da mishkila ta auku a tsakanin su.

Uwargidan Shugaba Buhari ta barrantar da kanta daga zargin rashawa

Uwargidan Shugaba Buhari ta barrantar da kanta daga zargin rashawa
Source: Depositphotos

Rahotannin sun bayyana cewa, wannan dambarwar ta biyo bayan yadda wasu ma'aikatan ofishin uwargidan shugaban kasa Buhari ke ribatar sunanta wajen zambace abokanan huldarsu ta kasuwanci.

Ko shakka ba bu wannan lamari ya sanya uwargidan shugaban kasa ta tsarkake kanta daga duk wata gudanarwa ta harkokin samun kudi domin kaucewa na shiga amma ban dauka ba.

KARANTA KUMA: Buhari zai jagoranci wani zaman Majalisa na musamman a ranar Juma'a

Majiyar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, Hajiya Aisha ta bayar da karfin gwiwa ga hukumomin tsaro na kasa wajen tabbatar da sauke nauyin da rataya a wuyansu na hukunta duk wani ma'aikacinta da aka damka da laifin zamba.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, a yau din dai ta Laraba, Hajiya Aisha ta bayyana yadda wasu jiga-jigai biyu na kasar nan da ba ta bayyana sunayensu be ke kawo cikas wajen samun nasarori ga gwamnatin Mai gidan ta.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel