APC na siyan katin zaben mutane - Atiku

APC na siyan katin zaben mutane - Atiku

Dan takaran kujeran shugaban kasan Najeriya karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ta zargi jam'iyyar All Progressives Congress APC na siyan kuri'u a farashi har N10.

Tsohon mataimakin shugaban kasan ya bayyana hakan ne a yau Laraba, 5 ga watan Disamba, 2018 a taron yakin neman zaben jam'iyyar PDP da aka gudanar a Ilori, jihar Kwara.

Yace: "A yau, mun ji gazawar gwamnatin APC daga shekarar 2015 zuwa yanzu. Babu irin alkawarin da basu yi mana ba, sunyi alkawarin tsaro, samar da ayyukan yi, karfin tattalin arziki, kuma duk sun fadi."

“Lokaci yayi domin mayar da Najeriya hannun PDP, saboda shekaru mafi albarka a tarihin kasar nan lokacin da PDP ke mulki tsakanin 199 da 2015 ne."

"A bangaren rashawa kuwa, abin ya fi tsanani a Najeriya fiye da shekarar 2014."

"Abinda APC ke yi shine. Suna saya katin neman zabe PVC. Za su zo wajenku suna baku N10, N20, N50 domin sayan katinku. Sun sayan rana gobenku ne."

Har yanzu, kakakin jam'iyyar APC bai mayar da martani kan wannan zargi ba.

KU KARANTA: Gobara ta tashi a gidan gwamnatin Benue, ta lalata muhimman abubuwa

Mun kawo muku rahoton cewa kungiyar hadin kan kungiyoyin siyasa CUPP da ta kunshi babbar jam'iyyar adawa ta PDP da sauran wasu jam'iyyun adawa 45 sun yanke hukuncin rike tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar a matsayin dan takarar su na shugaban kasa a zaben 2019 mai zuwa.

Shugaban kungiyar wanda kuma shine tsohon gwamnan jihar Osun, Prince Olagunsoye Oyinlola, ya bayyana hakan a ranar Laraba a Abuja, a bude taron shuwagabannin jam'iyyun na kasa.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel