Zolayar APC PDP keyi, bayan mukarrabin gwamnan Legas ya sauya sheqa

Zolayar APC PDP keyi, bayan mukarrabin gwamnan Legas ya sauya sheqa

- Jam'iyyar PDP ta bayyana barin Mista Wale Oluwo daga APC a matsayin cigaba

- Hakan na nuna cewa APC ba jam'iyyar mutane bace, inji Mista Taofeek Gani

- Oluwo makusanci ne ga gwamna Akinwunmi Ambode

Zolayar APC PDP keyi, bayan mukarrabin gwamnan Legas ya sauya sheqa

Zolayar APC PDP keyi, bayan mukarrabin gwamnan Legas ya sauya sheqa
Source: UGC

Jam'iyyar PDP ta Kwatanta barin tsohon kwamishinan wuta da ma'adanai na jihar Legas, Mista Wale Akinwunmi a matsayin cigaba.

Sakataren yada labarai na PDP a jihar Legas, Mista Taofeek Gani ne ya sanar da ofishin jakadancin labarai a ranar laraba cewa fitar Oluwo daga APC na nuna jam'iyyar ba ta mutane bace.

Ofishin dillancin labarai ya ruwaito cewa, Oluwo makusanci ne ga Gwamna Akinwunmi Ambode. Ya sanar da barin jam'iyyar ne a wasikar shi mai kwanan wata 3 ga Disamba.

DUBA WANNAN: Kisan jami'an tsaro a Arewa maso yamma, abin tsoro ne ko kuma tsohon lamari ne?

Yace ya bar jam'iyyar ne dalilin da yace na rashin damokaradiyyar cikin gida, wanda ya bayyana a zaben fidda gwanin da akayi a watan Octoba.

Daga baya Oluwo ya sanar da ofishin dillancin labarai cewa ya bar jam'iyyar shi ne don komawa jam'iyyar PDP domin ya yarda jam'iyyar adawar tana mutunta hakkokin damokaradiyya tare da ba wa mutane yanci.

Dama dai an sami sabani tsakanin jigogin APC a jihar, tun sanda jagaban su Tinubu ya kwace hanyar tazarce daga gwamna mai ci ya kawo Sanwo-Olu aka tsayar ya kuma kada gwamna Ambode a jihar. An tafka dirama Amma dole ya hakura.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel