Daya daga cikin hadiman gwamnan jihar Kogi ya yi murabus, ya fadi dalili

Daya daga cikin hadiman gwamnan jihar Kogi ya yi murabus, ya fadi dalili

Odaudu Jeol, babban mai taimakawa na musamman ga gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi a fannin sabbin kafafen yada labarai ya yi murabus daga matsayinsa nan ta ke.

Ya aike da wasikar murabus dinsa a ranar 5 ga watan Disambar 2018 ga gwamnan ta hannun Sakataren gwamnatin jihar ta Kogi.

Ya ce ya ajiye aikinsa ne saboda wani uzuri da ya taso masa na iyali.

Hadimin gwamnan jihar Kogi ya yi murabus

Hadimin gwamnan jihar Kogi ya yi murabus
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Har yanzu babu dan takarar shugaban kasa sahihi - Babban malamin addini

Wasikar ta ce: "Kamar yadda sashi na 306 na kundin tsarin mulkin Najeriya ta bukata. Ina mai juyayin sanar da kai cewa nayi murabus daga matsayi na na babban mai bawa shawara da gwamna a fannin sabbin kafafen yadda labarai saboda wasu dalilai na kashin kaina.

"Mai girma gwamna, na ajiye aiki na wannan lokacin ne saboda in samu damar warware wani abu da ya taso mani mai alaka da iyali na.

"Ina daya daga cikin tsirarin wadanda aka kafa wannan gwamnatin da su kuma na gudanar da ayyuka na cikin nagarta na kwarewa da dattaku ba tare da niyyar kawo wa gwamnatin ka cikas ba. Nayi matukar farin ciki kan yadda na ajiye aiki na ba tare da janyo maka wata matsala ba.

"Ina godiya ga mai girma gwamna saboda damar da ya bani na aiki a karkashinsa.

"Kazalika, ina mika godiya ta ga shugaban ma'aikatan jiha, Hon. Edward Onoja saboda shine ya yi min hanyar samun wannan damar da na bayar da gudunmawa ta ga wannan gwamnatin.

"Ina maka fatan alkhairi da mutanen jihar Kogi baki daya."

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel