Albashi ne zai nuna alkiblar ma'aikata a zaben 2019 - Kungiyar Kwadago

Albashi ne zai nuna alkiblar ma'aikata a zaben 2019 - Kungiyar Kwadago

Kungiyar Kwadago na kasa (NLC) ta ce karin mafi karancin albashi da ma'aikata ke nema gwamnatin Najeriya tayi zai taka muhimmiyar rawa wajen kada kuri a babban zaben shekarar 2019.

Daily Trust ta ruwaito cewa Sakatare Janar na kungiyar, Dr Pter ozo-Eson ne ya furta hakan a zantawa da ya yi da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a ranar Laraba a Abuja.

Ozo-Eson ya ce jinkirin da shugaba Muhammadu Buhari ya keyi na aike wa majalisar tarayya kudirin amincewa da karin alabashin zuwa N30,000 saboda a fara aiwatar da shi na iya sauya ra'ayoyin ma'aikata yayin kada kuri'a.

Rashin karin albashi zai iya janyo wa Buhari cikas a zaben 2019 - NLC

Rashin karin albashi zai iya janyo wa Buhari cikas a zaben 2019 - NLC
Source: Depositphotos

"Idan har ba a warware batun karin albashi mafi karanci a yanzu ba, batun zai taka muhimmiyar rawa kan yadda ma'aikata za su kada kuri'unsu a babban zaben 2019.

DUBA WANNAN: Har yanzu babu dan takarar shugaban kasa sahihi - Babban malamin addini

"Ina ganin ya kamata gwamnati tayi maza ta mayar da hankali kan batun albashi kada ya rincabe da babban zaben da za ayi a kasar," inji shi.

Ozo-Eson ya ce yanzu kusan mako guda kenan da kwamitin da shugaban kasa ya kafa domin nazarin karin alabashin karkashin Ama Pepple ya mika rahotonsa ga shugaban kasa inda ya shawarci a biya N30,000.

"Fiye da makonni uku kenan da kwamitin ta mika rahoton ta ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma ya yi alkawarin zai dauki mataki a kan rahoton cikin gaggawa.

"Abin na daure mana kai yadda har yanzu bai aike da kudirin karin albashin ga majalisar tarayya ba.

"Saboda haka, shawarar mu itace a tsige dukkan shugabanin da ke cikin gwamnati da suka nuna halin ko in kula game da walwalar ma'aikata ko kuma suka matsawa ma'aikatan.

"Mun fadawa 'ya'yan kungiyar mu suyi amfani da katin zabensu su tsige irin wannan mutanen," inji shi.

Jagoran na NLC ya ce tun shekaru biyu da suka gabata ya dace ayi karin albashin, ya kara da cewa ko da yake kasar na fuskantar wasu kallubalai na tattalin arziki, duk da haka gwamnati za ta iya tabbuka wani abu idan har ta damu da ma'aikatan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel