Ku rage albashinku, ya yi yawa gaskiya - Babban Sarki ya fadawa sanatocin Najeriya

Ku rage albashinku, ya yi yawa gaskiya - Babban Sarki ya fadawa sanatocin Najeriya

Sarkin Legas, Rilwan Akiolu ya yi kira ga sanatocin Najeriya su yiwa Allah su rage albashinsu da alawus-alawus din da suke karba duk wata saboda a cewarsa kudin ya yi yawa.

Ya yi wannan rokon ne bayan a kwanakin baya wani Sanata ya bayyana cewa shi da takwarorinsa na karbar Naira miliyan 13.5 a duk wata a matsayin kudin tafiyar da harkokinsu.

Sarkin ya yi wannan jawabin ne wajen wani taron jin ra'ayin al'umma kan yin garambawul a kan dokar 'yan sanda inda Mr Akiolu ya ce sojojin Najeriya sun dakushe ayyukan 'yan sanda kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Ku rage albashinku, ya yi yawa gaskiya - Babban Sarki ya fadawa sanatocin Najeriya

Ku rage albashinku, ya yi yawa gaskiya - Babban Sarki ya fadawa sanatocin Najeriya
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Har yanzu babu dan takarar shugaban kasa sahihi - Babban malamin addini

"Hukumar Sojin Najeriya ne ta janyo koma bayar 'yan sanda," inji sarkin sai dai bai yi karin bayani a kan abinda ya ke nufi da hakan ba.

Da ya cigaba da bayani, Sarkin ya ce matsalolin da ke adabar'yan sandan Najeriya sun hada da karancin albashi da fansho, rashin horaswa, katsalandan da gwamnati keyi cikin harkokin hukumar da kuma halaye marasa kyawu da kananan 'yan sanda ke dashi.

Ya shawarci gwamnatin Najeriya ta bukaci kamfanonin kasashen waje su rika bayar da wani tallafi ga 'yan sanda a matsayin aikinsu da more rayuwa da al'ummar Najeriya.

"A lokacin da na tafi karo ilimi a shekarar 2000, na bayar da shawara a cikin kasida ta cewa a ware wani kaso cikin ribar da kamfanonin kasashen waje ke samu domin tallafawa 'yan sanda." inji shi.

Mr Akiolu wadda tsohon sufeta janar na 'yan sanda ne ya ce yana goyon bayan shugaban kasa ya rika zaban wanda ya ke son ya zama IG ba tare da majalisar dattawa ta amince da shi ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel