Kamar dai arewa maso gabas, maso yamma ma ta fara asarar jami'an tsaro ga ta'addanci

Kamar dai arewa maso gabas, maso yamma ma ta fara asarar jami'an tsaro ga ta'addanci

- Yan sanda 16 ne suka rasa rayukan su a yayin wata karawa da akayi a 29 ga watan Nuwamba

- A wani bangaren kuma sun samu nasarar ceto yan sanda 20

- Rahoton ya bayyana cewa maharan 104 ne suka rasu

Kamar dai arewa maso gabas, maso yamma ma ta fara asarar jami'an tsaro ga ta'addanci

Kamar dai arewa maso gabas, maso yamma ma ta fara asarar jami'an tsaro ga ta'addanci
Source: Depositphotos

Yan sanda a jihar Zamfara sun bayyana cewa sun samu gawarwakin ma'aikatan su 16 yayin da wasu da dama suka bace.

A yayin wannan kalu bale sun samu nasarar tseratar ta wasu yan sanda su 20 wadanda suke hannun yan ta'addan.

Rahoton ya bayyana cewa inspector general na yan sanda Ibrahim Idris ya bada umarnin a binne gawarwakin wadanda suka rasu sannan a biya iyalan su diyyar su.

A ranar 29 ga watan Nuwamba ne dai maharan sukayi wa jami'an tsaron kwantan bauna a Birnin Mogaji dake Zurmi wata karamar hukumar jihar.

DUBA WANNAN: Baya ga suratu fatiha da Dino Melaye ya biya, PDP tayi kira ga talakawa su tashi da addu'a da azumin neman sa'a

Yan sandan sun bayyana cewa a yayin wannan karawar sun samu nasarar kashe yan ta'adda 104.

Sama da shekara kenan makiyaya suke tada tarzoma a jihar Zamfara da Katsina inda suke kashe rayukan da basuji ba basu gani ba wanda har zuwa yanzu jami'an tsaro da gwamnati basu samu damar kawo karshen lamarin ba.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel