Mulkin APC fa mun zarce mun gama, kada gabanku ya fadi, inji shugaba Buhari ga Najeriya

Mulkin APC fa mun zarce mun gama, kada gabanku ya fadi, inji shugaba Buhari ga Najeriya

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya hori magoya bayan shi da kada su tsorata

- Ya kwatanta masu son saukar shi daga kujerar shugabancin kasa a matsayin makiyan kasa

- Burin su shine sace kudin kasa kuma dole mu hana su

Ya hallaka kansa garin kokarin zulle wa jami'an tsaro ya tsunduma ruwa

Ya hallaka kansa garin kokarin zulle wa jami'an tsaro ya tsunduma ruwa
Source: Twitter

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya hori magoya bayan shi da kada su tsorata. Akwai yuwuwar dawowar shi kujerar shi.

Ya Kwatanta wadanda ke so saukar shi daga kujerar shi a zabe mai gabatowa a matsayin makiyan kasa masu burin wawure dukiyar kasa.

Ya bayyana hakan ne a zauren kwamitin kungiyoyin goyon bayan Buhari a Abuja.

DUBA WANNAN: An sa a kamo mai takarar gwamna a Taraba a APC

Buhari, wanda mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya wakilta ya Kwatanta cigaban ababen more rayuwa, yaki da rashawa da ciyar da yan makaranta a cikin nasarorin da suka kara soyayyar shugaban ga mutane.

Yayi mamakin dalilin da yasa PDP wacce ake zargi da watanda da dukiyar kasa zata so komawa mulki a 2019.

Manyan baki a wajen taron sun hada da Bola Ahmed Tinubu, shugaban jam'iyyar APC, gwamnan jihar Legas, Akinwumi Ambode da sanatoci George Akume, Ayogu Eze da Abu Ibrahim.

Tinubu yayi alkawarin APC zata yi wa PDP warwas.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel