Yanzu-yanzu: An yi garkuwa da likitoci da ma'aikacin asibiti

Yanzu-yanzu: An yi garkuwa da likitoci da ma'aikacin asibiti

Ma'aikatan asibitin gwamnatin tarayya da ke garin Owo, jihar Ondo sun shiga hannun masu garkuwa da mutane a yau Laraba, 5 ga watan Disamba, 2018.

Wadanda wannan abu ya shafa sune likita, likita mace, da kuma wani ma'aikaci. Anyi garkuwa da su ne yayinda suka taso daga babbar birnin jihar, Owo.

Wani abokin aikinsu wanda yayi hira da tashar Channels ya bayyana cewa masu garkuwa da mutanen sun bukaci N50,000 matsayin kudin fansansu.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Femi Joseph, ya tabbatar da wannan labari kuma ya ce hukumar ta kaddamar da bincike kan al'amarin.

Cikakken rahoton......

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel