Buhari zai jagoranci wani zaman Majalisa na musamman a ranar Juma'a

Buhari zai jagoranci wani zaman Majalisa na musamman a ranar Juma'a

Za ku ji cewa, a wannan mako shugaban kasa Muhammadu Buhari, zai jagoranci wani muhimmin zaman majalisa na musamman domin aiwatar da shirye-shirye na gabatar da kasafin kudin 2019 kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito.

Kakakin shugaban kasa, Mista Femi Adesina, shine ya bayyana hakan yayin ganawarsa da manema labarai na fadar shugaban kasa bayan zaman majalisar zantarwa da ya gudana a yau Laraba.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, a yau Laraba, Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, shine ya jagoranci zaman majalisar da ya gudana cikin fadar shugaban kasa ta Villa da ke babban birnin kasar nan na tarayya.

Mista Adesina ya bayyana cewa, zaman majalisar na musamman da za ya gudana a ranar Juma'a karkashin jagorancin shugaba Buhari, za ya tattauna kan al'amurran da suka shafi sabon kasafin kudin 2019 domin gabatar da shi zuwa ga Majalisar dokoki ta tarayya.

Buhari zai jagoranci wani zaman Majalisa na musamman a ranar Juma'a

Buhari zai jagoranci wani zaman Majalisa na musamman a ranar Juma'a
Source: Depositphotos

Rahotanni kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito sun bayyana cewa, akwai kyakkyawon zato dangane da samun inganci da habakar tattalin arzikin kasar nan duba da yadda ake hasashen kasafin kudin badi na kasar nan za ya kasance.

KARANTA KUMA: Babbar Magana: An yi garkuwa da wani Manomi a jihar Gombe

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, a ranar 18 ga watan Oktoba da ya gabata Ministan kasafi tsare-tsaren kasa, Udoma Udo Udoma ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta kudirci gabatar da kasafin kudin kasar nan na badi zuwa ga Majalisar tarayya gabanin shudewar watan Nuwamba.

Kazalika jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa cikin sauki za ya kawo karshen ta'addanci Boko Haram a Najeriya ta hanyar Diflomasiyya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel