2019: Alamomi 7 dake nuna cewar gwamnonin yankin kabilar Igbo na tare da Buhari

2019: Alamomi 7 dake nuna cewar gwamnonin yankin kabilar Igbo na tare da Buhari

An dade ana cece-kuce a kan bangaren da ra'ayin gwamnonin yankin kudu maso gabas na 'yan kabilar Igbo ya rinjaya dangane da goyon bayan dan takarar kujerar shugaban kasa tsakanin Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP da shugaba Buhari na jam'iyyar APC.

Yankin kudu maso gabas na da jihohi guda 5; Abiya, Anambra, Ebonyi, Enugu, da Imo. Daga cikin jihohin 5, PDP na da gwamnoni 3; Abiya, Anambra, da Ebonyi, APC na da gwamna 1; jihar Imo, sai jam'iyyar APGA da ita ma keda jiha 1; jihar Anambra.

A yayin da zaben shekarar 2019 ke kara matsowa, alamomi na kara bayyana cewar gwamnonin PDP da jiga-jigan 'ya'yan jam'iyyar daga yankin basa tare da Atiku, dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam'iyyar PDP.

Legit.ng ta tattara wasu alamomi na zahiri dake nuna cewar gwamnoni da manyan 'yan siyasar yankin na goyon bayan tazarcen Buhari a karkashin inuwar jam'iyyar APC.

1. Ziyarar gwamnonin yankin ga Buhari: A 'yan kwanakin baya bayan nan ne gwamnonin yankin kudu maso gabas tare da mataimakin shugaban majalisar dattijai Sanata, Ike Ekweremadu, su ka ziyarci Buhari a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Batun ziyarar ya kara tabbatar wa da jama'a cewar akwai wata siyasa a karkashin kasa tsananin gwamnonin da shugaba Buhari.

2019: Alamomi 7 dake nuna cewar gwamnonin yankin kabilar Igbo na tare da Buhari

Gwamnonin yankin kabilar Igbo tare da Buhari
Source: UGC

2. Kauracewa bikin nadin sarautar Atiku: Wani abu da ya kara haska wa jama'a inda gwamnonin yankin kudu maso gabas suka sa gaba, shine yadda bakidayansu suka kauracewa bikin nadin Atiku a matsayin wazirin Adamawa.

Bayan rashin halartar taron, gwamnonin basu aike da wakilci ko sakon taya murna ga Atiku ba.

3. Nuna shakku a kan alkawura da manufofin kamfen din Atiku: Tun bayan da Atiku ya fitar da manufofin yakin zabensa 'yan kabilar Igbo suka fara nuna shakku a kan alkawarin cewar zai yi zango daya ne kawai a mulki.

Manya da kananan 'yan siyasar kabilar Igbo sun ce alkawuran da Atiku ya dauka a cikin manufar yakin neman zabensa sun nuna zasu kammalu ne cikin shekara 6, a saboda haka batun zai yi zango daya ya mika mulki ga yankin, duk romon baka ne.

DUBA WANNAN: Jerin sunaye: Rundunar soji ta samu sabbin Manjo Janar 29, Birgediya janar 95

4. Kalaman yabon Buhari na gwamna Ifeanyi Ugwuanyi: Gwamnan jihar Enugu, Ifeanyi Ugwuanyi, ya sha fitowa fili ya yabi shugaba Buhari.

Ko a yanzu haka, Ugwuanyi na daga cikin tawagar jami'an gwamnatin Najeriya da suke tare da Buhari a ziyarar aiki da yake yi a kasar Poland.

Ba batun raka Buhari ne kadai ya jawo cece-kuce a kan Ugwuanyi ba, a daya daga cikin hotunansa tare da Buhari a kasar Poland, an ga gwamnan makale da bajon kamfen din Buhari a jikin rigar sa.

5. Soyayyar da Umahi ke nunawa Buhari: Ko a watanni baya sai da rahotanni suka bayyana cewar gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya koma jam'iyyar APC. Duk da Umahi ya musanta hakan, rahotannin sun wallafa rahoton canjin shekar tasa ne bisa ganin yadda ko da yaushe yake nuna kaunar sa ga shugaba Buhari tare da yabon kokarinsa, musamman a bangaren yaki da cin hanci da rashawa.

Gwamna Umahi ba ya boye adawar sa ga dan takarar mataimakin shugaban kasa a karkashin inuwar jam'iyyar PDP, Peter Obi.

6. Rigimar siyasa dake tsakanin gwamna Obiano da Peter Obi: Masu bibiyar al'amuran siyasar jihar Anambra sun tabbatar da cewar ko kato bayan kato za a yi, gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano, bayan Buhari zai bi saboda yadda ba a ga maciji tsakaninsa da tsohon gwamnan jihar kuma dan takarar mataimakin shugaban kasa a PDP, Peter Obi.

Duk da Obiano dan jam'iyyar APGA ne dake da dan takarar ta na shugaban kasa, hankalin gwamnan ya fi karkata zuwa ga Buhari.

7. Jawabin gwamna Okezie Ikpeazu: Bayan gwamnonin yankin kudu maso gabas sun kammala ganawa da shugaba Buhari, gwaman jihar Abiya, Okezie Ikpeazu, ta bakin sakatarensa na yada labarai, Enyinnaya Appolos, ya fitar da jawabin yabo da begen shugaba Buhari. Faruwar wannan lamari ya kara tabbatar da cewar gwamnonin jam'iyyar PDP a daga yankin 'yan kabilar Igbo basu da niyyar marawa PDP da Atiku baya domin su samu kuri'un jama'ar yankin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel