Furucin Aisha ya nuna cewa wasu ke tafiyar da gwamnatin Buhari – Kungiyar Atiku

Furucin Aisha ya nuna cewa wasu ke tafiyar da gwamnatin Buhari – Kungiyar Atiku

Kungiyar kamfen din Atiku Abubakar sun yaba ma uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari kan amincewa da tayi cewa wasu mutane biyu ke ciwa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari dunduniya.

Kungiyar tace furucin Aisha hujja ce na cewa wasu ke tafiyar da gamnatin Buhari.

Da farko dai Uwargidan shugaban kasar ta yi bayanin cewa gwamnatin mai gidanta ta samu nasarori da dama amma da nasarorin sun fi haka idan ba don wadannan mutane biyu da ke gwamnatin ba wanda basa bari abubuwa su tafi cikin sauri.

Uwargidan shugaban kasar ta bayyana cewa wasu maza sun bata kunya domin a maimakon su yaki wadannan mutane biyu sai su bi dare su je rokon alfarma a wurinsu.

Furucin Aisha ya nuna cewa wasu ke tafiyar da gwamnatin Buhari – Kungiyar Atiku

Furucin Aisha ya nuna cewa wasu ke tafiyar da gwamnatin Buhari – Kungiyar Atiku
Source: Facebook

Da yake zantawa da manema labarai a ranar Laraba, 5 ga watan Disamba, kakakin kungiyar kamfen din Atiku, Mista Segun Sowunmi yace a bayyane yake karara cewa wasu ne ke yin yadda suka so a gwamnati mai mulki.

KU KARANTA KUMA: Aisha ta fadi wasu manya 2 a Najeriya dake dakile kokarin Buhari

“Hakan na fin cewa bai da iko a kasar, lallai ashe shiyasa jirgin ragamar abubuwan kasar ke ta nanaye a kan kogi, shiyasa rundunar tsaro da tattalin arziki suka kasa ci gaba sannan ga tarin talauci.”

Sowunmi yace uwargidan Buhari ta fi kowa hikima a sansanin Buhari.

Ya kuma bukaci Aisha da ta ci gaba da tona asirin wadanda ke cin dunduniyar gwamnatin Buhari, har ya bata shawara da ta shawo kan mijinta da kada yayi takara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel