Zan kawo karshen Boko Haram ta hanyar diflomasiyya - Atiku Abubakar

Zan kawo karshen Boko Haram ta hanyar diflomasiyya - Atiku Abubakar

- Atiku Abubakar, ya ce daya daga cikin muhimman kudurorin gwamnatinsa, shine samar da 'AIKI' ta hanyar bunkasa noma da manya da matsakaitun masana'antu

- Haka zalika, Atiku ya bayyana cewa, idan har 'yan Nigeria suka zabe shi a 2019, zai kawo karshen tashin hankula da matsalar tsaro da ke addabar kasar

- Ya kuma jaddada cewa zai nemi tallafin masu rike da sarautun gargajiya a wajen kawo karshen ta'addancin Boko Haram

A yayin da tawagar yakin zaben dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP ta isa jihar Kwara, Atiku Abubakar, ya ce daya daga cikin muhimman kudurorin gwamnatinsa, shine samar da 'AIKI' ta hanyar bunkasa noma da manya da matsakaitun masana'antu na kasar.

Haka zalika, Atiku ya bayyana cewa, daga cikin muhimman kudoririn gwamnatin tasa idan har 'yan Nigeria sun zabe shi a 2019, akwai kawo karshen tashin hankula da matsalar tsaro da ke addabar kasar.

KARANTA WANNAN: 2019: Ma damar ba'ayi magudi ba, APC ba zata iya lashe zabe ba - tsohon hadimin Jonathan

Zan kawo karshen Boko Haram ta hanyar diflomasiyya - Atiku Abubakar

Zan kawo karshen Boko Haram ta hanyar diflomasiyya - Atiku Abubakar
Source: Twitter

Dan takar shugaban kasar karkashin PDP ya ce zai kawo karshen rikicin makiya da manoma, ta'addancin mayakan Boko Haram, garkuwa da mutane, da dai sauransu, "ta hanyar amfani da kwarewar tunani da mutane, bunkasa alakar tsaron iyakar kasa da kuma uwa uba, amfani da diflomasiyya."

Haka zalika, Atiku Abubakar ya ce nasarar hakan ba zata taba samuwa ba har sai an shigo da masu rike da sarautun gargajiya na kasar don suma su bada tasu gudunmowar, musamman ganin cewa masu rike da sarautun gargajiya na daga cikin wadanda gwamnatinsa zata fi maida hankali kansu.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel