Yanzu Yanzu: Fayose ya yi hatsari a gadar Third Mainland

Yanzu Yanzu: Fayose ya yi hatsari a gadar Third Mainland

- Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya yi hatsari a gadar Third Mainland da ke jihar Lagas

- Hadiminsa, Lere Olayinka ya tabbatar da hatsarin a shafinsa na twitter

- Ya ce yana samun kulawar likitoci da sauki sosai

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose a ranar Talata, 5 ga watan Disamba ya yi hatsari a gadar Third Mainland da ke jihar Lagas, jaridar Punch ta ruwaito.

Yanzu Yanzu: Fayose ya yi hatsari a gadar Third Mainland

Yanzu Yanzu: Fayose ya yi hatsari a gadar Third Mainland
Source: Depositphotos

Mai bashi shawara a kafofin watsa labarai, Lere Olayinka ya bayyana hatsarin a shafinsa na twitter.

Ya kuma bayyana cewa Fayose na nan lafiya kuma yaa samun kulawar likita.

KU KARANTA KUMA: Aisha ta fadi wasu manya 2 a Najeriya dake dakile kokarin Buhari

Ya rubuta: “Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Mista Ayodele Fayose ya yi hatsari a gadar 3rd Mainland da ke Lagas yan mintuna kadan da suka wuce. Yana cikin yanayi mai kyau a yayinda nake wannan rubutun yana samun kulawar likita.”

Hatsarin ya faru ne yayinda yake cikin motarsa kirar G-Wagon Benz mai lamba AAA777TM.

Ya kuma shafi wata mota kirar Toyota Avalon mai lamba FKJ643DR.

Koda dai babu wanda yamutu a tattaro cewa gilashin motan da suka farfashe sun shiga jikin Fayose.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel