Bizan Amurka: Kungiyoyi 200 masu zaman kansu sun yi zanga-zanga akan Atiku a Abuja

Bizan Amurka: Kungiyoyi 200 masu zaman kansu sun yi zanga-zanga akan Atiku a Abuja

Sama da kungiyoyi masu zaman kansu 200 sun mamaye ofishin jakadancin Aurka a ranar Laraba, 5 ga watan Disamba don yin zanga-zanga akan bizar shiga kasar da aka baiwa tsohn mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyya Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar wanda gwamnatin Amurka ta yi.

Kungiyar ta bukaci gamnatin Amurka da kada ta bashi biza saboda zargin rashawa da ake masa, musamman yanzu da zaben 2019 ke kara gabatowa.

Kungiyar sun kasance da kwalayen sanarwa daban-daban inda suka rubuta: “Satar kudi shine mafi girman laifi da mutun zai aikata.

Bizan Amurka: Kungiyoyi 200 masu zaman kansu sun yi zanga-zanga akan Atiku a Abuja

Bizan Amurka: Kungiyoyi 200 masu zaman kansu sun yi zanga-zanga akan Atiku a Abuja
Source: Depositphotos

"Amurka, kada ki amince dsa bukatar bzan Atiku; yan Najeriya kada ku yarda a shiga siyasar kasar; mun samu wasika daga Amurka inda ta bayyana mutane da ake bincike aka satar kudi, Atiku na daya daga cikinsu.

"Amurka dan Allah kada ki sanya baki a siyasar Najeriya; kada a ba Atiku bizan siyasa, mme yasa sai yanzu bayan shekaru 14 da aka hana shi saboda satar kudi."

KU KARANTA KUMA: Bukola Saraki ya nemi ayi maza a biyawa Ma'aikatan Majalisa bukatun su

Shugaban kungiyar na kasa, Kwamrad Wole Badmus, wanda yayi jawabi ga manema labarai ya roki gwamnatin Amurka da ta jajirce sannan ta tabbatar da anyi zabe n gaskiya a Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel