Da dumi dumi: Jam'iyyun siyasa 45 sun goyi bayan takarar Atiku Abubakar na PDP

Da dumi dumi: Jam'iyyun siyasa 45 sun goyi bayan takarar Atiku Abubakar na PDP

Kungiyar hadin kan kungiyoyin siyasa CUPP da ta kunshi babbar jam'iyyar adawa ta PDP da sauran wasu jam'iyyun adawa 45 sun yanke hukuncin rike tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar a matsayin dan takarar su na shugaban kasa a zaben 2019 mai zuwa.

Shugaban kungiyar wanda kuma shine tsohon gwamnan jihar Osun, Prince Olagunsoye Oyinlola, ya bayyana hakan a ranar Laraba a Abuja, a bude taron shuwagabannin jam'iyyun na kasa.

KARANTA WANNAN: Cin amana tsagoransa: Wata mata ta shaidawa mijinta cewa ba shine uban 'yayansu 3 ba

Da dumi dumi: Jam'iyyun siyasa 45 sun goyi bayan takarar Atiku Abubakar na PDP

Da dumi dumi: Jam'iyyun siyasa 45 sun goyi bayan takarar Atiku Abubakar na PDP
Source: Facebook

A wani labarin; Kungiyar 'The All Progressives Congress (APC) Solidarity Group', reshen jihar Ondo ta yi ikirarin cewa akwai wasu jigogin jam'iyyar a jihar da ta gano suna kulla makirci don dakile shugaban kasa Muhammadu Buhari daga yin tazarce a babban zaben 2019.

Gbenga Bojuwomi, shugaban kungiyar a jihar ya yhi wannan zargin a lokacin da yake xantawa da manema labarai a sakatariyar APC ta kasa a ranar Talata, 03 ga watan Disamba, a Abuja.

KARANTA WANNAN: 2019: Wata kungiya tayi zargin cewa akwai jigogin APC da ke adawa da tazarcen Buhari

Ya ce kungiyar zuwa yanzu na da kwararan hujjoji na wannan zargi nata. Ya kuma ce ba sau daya ba sau biyu ba, jigogin jam'iyyar ke gudanar da taron sirri kan wannan kuduri nasa kuma suna aikiwa wata jam'iyyar hamayya.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel