Kan kungiyar dattawan Arewa ya rabe biyu kan Buhari

Kan kungiyar dattawan Arewa ya rabe biyu kan Buhari

A jiya Talata, rahotanni sun bayyana cewa da alamun rikici ya kunno kai a kungiyar dattawan Arewacin Najeriya wato NEF kan goyon bayan shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2019.

Yayinda sashe daya karkashin jagorancin Sani Zangon Daura(Danmasanin Daura), Manjo Janar Paul Tarfa, da Capt Bashir Sodangi, suka marawa shugaba Buhari baya, shugaban kungiyar Farfesa Ango Abdullahi ya ce har yanzu basu yanked an takaran shugaban kasan da zasu zaba ba.

Farfesa Ango Abdullahi ya bayyanawa jaridar Leadership cewa Dan masanin Daura, Tarfa da Sodangi basu da hurumin Magana da sunan kungiyar .

Ya ce kungiyar bata tabbatar da Buhari a matsayin wanda zata goyawa bay aba a zaben 2019.

Su (Daura, Tarfa da Sodangi) kuma sun saki jawabi domin watsi da da maganan Ango Abdullahi.

KU KARANTA: Kwamandan jami’an Peace corp, mambobi 6000 sun sauya sheka daga jam’iyyar APC

A cewarsu. Babu adalci a yi tunanin gwamnatin Buhari ta magance matsalolin da gwamnatin baya ta gaza cikin shekaru 3. Saboda haka, suna goyon bayan Buhari domin zaman lafiya, shugabanci na kwarai da cigaban kasa.

Wasu kungiyoyi 59 dake goyan bayan mulkin Shugaban kasa Muhammad Buhari sunyi tawaye sun koma bayan Atiku Abubakar.

Shugaban kungiyar ta Grassroots Mobilisers Yusuf Musa Ardo ya bayyana canjin da sukayi a maimakon kungiyoyin 59 a ranar Litinin a Abuja.

Ardo ya bayyana dalilin su na barin goyawa shugaba Buhari baya suka komawa Atiku.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel