Kwamandan jami’an Peace corp, mambobi 6000 sun sauya sheka daga jam’iyyar APC

Kwamandan jami’an Peace corp, mambobi 6000 sun sauya sheka daga jam’iyyar APC

Rikicin da ya dabibaiye jam’iyyar All Progressives Congress, APC, a jihar Benue ya dau sabon salo yayinda shugaban jami’an Peace Corp kuma jigon jam’iyyar APC, Cif Dickson Akor, ya sauya sheka daga jam’iyyar zuwa jam’iyyar SDP.

Komawarsa jam’iyyar Social Democratic Party SDP ke da wuya aka bashi kujeran takaran mataimakin gwamnan jihar a zaben 2019.

Fitar Akor daga jam’iyyar ta kawo baraka cikin shugabancin jam’iyyar APC a jihar inda kakakin jam’iyyar Peterhot Apeh, ya mika takardan murabus dinsa.

KU KARANTA: An rantsar da sabbin yan majalisan wakilai 3, duka yan APC

Bayan haka mambobin jam’iyyar akalla 6,000 sun sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa PDP a garin Tine-tine. Karamar hukumar Ukum da ke jihar Benue.

Yayinda manema labarai suka tuntubi Akor, ya tabbatar da cewa lallai ya bar jam’iyyar APC saboda irin cin mutuncin da akayi masa lokacin zaben dan takaran mataimakin gwamnan jihar.

Jam’iyyar APC a jihar Benue ya fara samin matsala ne tun lokacin da gwamnan jihar Samuel Ortom, ya koma PDP. Ortom ya bayyana cewa dalilin komawarsa shine wani jigon jam’iyyar, Sanata George Akume, na yi masa kora da hali daga jam’iyar.

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel