Yanzu Yanzu: Kwamishinan Ambode ya yi murabus daga APC

Yanzu Yanzu: Kwamishinan Ambode ya yi murabus daga APC

Kwamishinan ma’adinai na jihar Lagas, Mosta Olawale Oluwo ya sanar da sauya shekarsa daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Mista Oluwo ya sanar da hakan ne a wasikar murabus da ya aike wa gidan talbijin din Channels.

A wasikar kwanan wata 3 ga watan Disamba zuwa ga shugaban APC a jihar, yayi bayanin cewa ya yanke shawarar yin murabus ne samakon dukkanin abunda ya faru a zabe fidda gwani a jam’iyyar wanda ya gudana a wata Oktoba.

Yanzu Yanzu: Kwamishinan Ambode ya yi murabus daga APC

Yanzu Yanzu: Kwamishinan Ambode ya yi murabus daga APC
Source: Depositphotos

Oluwo ya yi zargin cewa zaben na cike a rikici, tauye hakkin masu zabe, razana mambobin jam’iyya da sauran ayyukan da suka saba ma dokar zabe.

KU KARANTA KUMA: Bukola Saraki ya nemi ayi maza a biyawa Ma'aikatan Majalisa bukatun su

Ya kuma yi ikirarin cewa jam’iyyar bata da mutunci, inda ya bayyana cwa hakan ya bata sunan jihar a matsayinta na cibiyar zabe mai inganci da damokradiyya.

Har yanzu dai shgaban APC a jihar bai mayar da martani ga zargn kwisinan ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel