Da duminsa: An rantsar da sabbin yan majalisan wakilai 3, duka yan APC

Da duminsa: An rantsar da sabbin yan majalisan wakilai 3, duka yan APC

Kakakin majalisan wakilan Najeriya, Yakubu Dogara, ya rantsar da sabbin yan majalisa da suka lashe zaben maye gurbin mazabarsu a majalisan wakilan tarayya da ke Abuja a yau Laraba, 6 ga watan Disamba 2018.

Dukkan wadannan yan majalisun yan jam'iyya mai ci ta All Progressives Congress APC ne.

Sabbin yan majalisun sune Yusuf Nuhu mai wakiltan mazabar Bauchi da Toro, Tuni Olawuyi mai wakiltan mazabar Kwara, Irepodun/Isin/Oke Ero/Ekiti a jihar Kwara, da Abubakar Kusada mai wakiltan mazabar Katsina, Kankia/Kusada.

KU KARANTA: Asirce-asirce: Hukumar yan sanda ta alanta fito-na-fito da bokaye – AIG Lawal

An rantsar da su domin maye gurbin mazabar jihar Katsina da Bauchi sakamakon komawan yan majalisan dake rike da kujerun majalisar dattawa. Sanata Kaita da Sanata Lawal Gumau sun koma majalisar dattijan domin maye gurbin sanatocin da suka rasu.

Shi kuma na jihar Kwara, ya maye gurbin yar majalisa Funke Adedoyi, da ta mutu a watan Satumba bayan gajeruwar rashin lafiya.

Mun kawo muku rahoton cewa dan majalisan wakilan jam'iyyar APGA, Gabriel Onyewife, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar adawa ta PDP a yau Laraba a zauren majalisa.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel