Rundunar soji ta tabbatar da mutuwar jami'anta 8 a harin Boko Haram

Rundunar soji ta tabbatar da mutuwar jami'anta 8 a harin Boko Haram

Rundunar sojin Najeriya a ranar Talata, 4 ga watan Nuwamba ta tabbatar da mutuwar sojoji takwas a wani hari da yan ta’addan Boko Haram suka kai sansanin sojoji a karshen mako a yakin arewa maso gabashin kasar, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Yan ta’addan sun kai hari a sansanin soji da ke kauyen Buni Gari da ke jihar Yobe a ranar Asabar.

Majiyar soji da fari ta bayyana cewa sojoji biyu da yan ta’adda shida aka kashe. A safiyar ranar Talata, 4 ga watan Disamba sai suka fadama AFP cewa yawan sojojin da suka mutu ya tashi zuwa takwas.

Rundunar soji ta tabbatar da mutuwar jami'anta 8 a harin Boko Haram

Rundunar soji ta tabbatar da mutuwar jami'anta 8 a harin Boko Haram
Source: UGC

Wani babban jami’in soja da ya nemi a boye sunansa domin ba’a bashi damar yin Magana ga kafofi watsa labarai bay ace an kwashi gawawwaki shida zuwa Damaturu, babbar birnin jihar Yobe.

KU KARANTA KUMA: Bukola Saraki ya nemi ayi maza a biyawa Ma'aikatan Majalisa bukatun su

Yan ta’addan sun kuma lalata motar bindiga sannan suka sace wata babbar mota a lokacin harin.

Majiyar ta bayyana cewa rundunar sojin sama daga sansaninsu na kusa da kauyen Buni Gari sun taimaka wajen fatattakan yan ta’addan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel