Yanzu Yanzu: Wani dan majalisar wakilai ya sauya sheka zuwa PDP

Yanzu Yanzu: Wani dan majalisar wakilai ya sauya sheka zuwa PDP

Mamba mai wakiltan mazabar Oyi/Anyamelum na Jihar Anambra a majalisar wakilai, Mista Gabriel Onyewinfe, ya sauya sheka daga jam’iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara ya karata wasika daga Onyewinfe a zauren majalisa a ranar Laraba, 5 ga watan Disamba inda ya sanar da sauya shekar nasa.

Yanzu Yanzu: Wani dan majalisar wakilai ya sauya sheka zuwa PDP

Yanzu Yanzu: Wani dan majalisar wakilai ya sauya sheka zuwa PDP
Source: Depositphotos

Onyenwinfe ya daura hakkin sauya shekar nasa akan sakamakon zaben fidda gwani da APGA ta yi a Anambra.

KU KARANTA KUMA: Aisha ta fadi wasu manya 2 a Najeriya dake dakile kokarin Buhari

Ya ce APGA na cikin gagarumin matsala sannan kuma cewa jam’iyyar ba ta bin tafarkin daokradiyya. Ya kuma bayyana cewa jam’iyyar ta rabe, inda aka sau sabuwar APGA.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel