Kaico! Yan bindiga sun bindige jami’an Yansanda 16 a jahar Zamfara, 20 sun ɓace

Kaico! Yan bindiga sun bindige jami’an Yansanda 16 a jahar Zamfara, 20 sun ɓace

Rundunar Yansandan jahar Zamfara ta tabbatar da kashe jami’anta guda goma sha shida (16) da tace yan bindiga da suka addabi jahar Zamfara ne suka kashesu, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Majiyar Legit.com ta ruwaito rundunar ta bayyana haka ne cikin wata sanarwar data fitar a ranar Talata 4 ga watan Disamba, inda tace an kashe Yansandan ne a wata artabu da aka kwasa tsakanin Yansanda da wasu gungun yan bindiga.

KU KARANTA: Yadda wani mutumi ya kashe kansa ta hanyar fada ma jirgin kasa a garin Abuja

Sanarwar ta kara da cewa rundunar ta samu nasarar ceto sauran Yansanda guda ashirin da suke bace a sakamakon harin da yan bindigan suka kai musu, sa’annan ta jaddada manufarta na kara kaimi wajen yakar yan bindigan.

A ranar 29 ga watan Nuwamba ne yan bindigan suka yi ma ayarin motocin Yansanda kwantan bauna a garin Binin Magaji dake cikin karamar hukumar Zurmi ta jahar Zamfara da misalin karfe 4 na rana, sai dai a wancan lokacin rundunar cewa ta yi Dansanda daya aka kashe, sai a yanzu ne gaskiyar ta bayyana.

Bayan rahotonta na farko, a ranar 2 ga watan Nuwamba ma rundunar Yansanda ta shaida ma majiyarmu cewa Yansanda hamsin (50) aka halaka a sanadiyyar harin, sa’annan tana kokarin kwaso gawarwakinsu. Da wannan ne dan takarar shugaban kasa Atiku Abubakar yayi kira a kaddamar da zaman makoki na kwanaki bakwai saboda kashe kashen yayi yawa.

Amma a cikin rahoton data fitar a ranar Talata, rundunar tace: “An gano Yansanda goma sha shida da aka kashe bayan harin ceto da rundunar Yansandan ta kai inda ta samu nasarar ceto jami’an Yansanda guda ashirin.

“Babban sufetan Yansandan Najeriya ya bada umarnin a yi musu jana’izar data dace dasu, tare da tabbatar da biyan iyalansu hakkokinsu cikin gaggawa, wannan shine sadaukarwar da suka yi don tabbatar da tsaro a Najeriya.” Inji sanarwar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel