Yadda wani mutumi ya kashe kansa ta hanyar fada ma jirgin kasa a garin Abuja

Yadda wani mutumi ya kashe kansa ta hanyar fada ma jirgin kasa a garin Abuja

Rundunar Yansanda babban birnin tarayya Abuja ta fara binciken bayanai da sunan wani bawan Allah daya kashe kansa ta hanyar fada ma wani jirgin kasa inda ya kwanta akan layin dogo a daidai lokacin da jirgin kasan yake cikin sharara gudu.

Majiyar Legit.com ta ruwaito ruwaito lamarin ya faru ne a yankin Phikwore na garin Kubwa dake babban birnin tarayya Abuja a ranar Litinin 3 ga watan Disamba. Sai dai Yansanda na danganta lamarin da yunkurin kashe kai ne.

KU KARANTA: Yansanda sun yi ram da maigadin makabarta ya kwakulo gawar mutum daga cikin kabari

Haka zalika rahotanni sun tabbatar da cewar mutumin mai matsakaicin shekaru yayi nufin kashe kanshi da kashi ne haka ne yasa ya kwanta akan layin dogo a daidai lokacin da yaga jirgin ya karato, nan take jirgin yayi fata fata dashi tare da yanka shi gunduwa gunduwa.

Yadda wani mutumi ya kashe kansa ta hanyar fada ma jirgin kasa a garin Abuja

Jirgi
Source: Depositphotos

DPO na Yansandan yankin Kubwa, CSP Surajudeen Ayobami ya tabbatar da faruwar lamarin, inda tace tuni aka tattara sauran dago dagon naman mutumin aka mikasu ga babban asibitin Kubwa. Sai dai yace sun gano wata wasika a cikin aljihunsa.

“Mun gano wata wasika a cikin aljihunsa dake bayyana dalilin da yasa ya kashe kansa, a cikin wasikar yayi ma Najeriya da yan Najeriya addu’a, haka zalika ya nemi iyalansa su gafarta masa saboda ya gaza wajen kulawa dasu, sa’annan ya rubuta lambar waya da za’a tuntuba.

“Amma mun yi ta kiran lambar ba ta shiga, duk da haka zamu cigaba da bin lambar har sai mun gano me ita, daga nan ne kuma zamu gane ko wanene mutumin nan daya kashe kansa.” Inji DPO Ayobami.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel