Aisha ta fadi wasu manya 2 a Najeriya dake dakile kokarin Buhari

Aisha ta fadi wasu manya 2 a Najeriya dake dakile kokarin Buhari

Uwargidan shugaban kasa, Dr. Aisha Buhari a ranar Laraba, 5 ga watan Disamba ta yi korafin cewa wasu manyan mutane biyu ne cin dunduniyar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da hana shi yin ayyukan ci gaba cikin sauri a kasar.

Aisha wacce tayi magana a wani taro da aka shirya a Abuja bata ambaci sunayen manyan mutanen ba.

Taron ya kuma samu halartan uwargidan mataimakin shugaban kasa, Dolapo Osinbajo.

Aisha ta fadi wasu manya 2 a Najeriya dake dakile kokarin Buhari

Aisha ta fadi wasu manya 2 a Najeriya dake dakile kokarin Buhari
Source: Depositphotos

Uwargidan shugaban kasar ta yi bayanin cewa gwamnatin mai gidanta ta samu nasarori da dama amma da nasarorin sun fi haka idan ba don wadannan mutane biyu da ke gwamnatin ba wanda basa bari abubuwa su tafi cikin sauri.

KU KARANTA KUMA: 2019: Atiku zai garzaya da kamfen dinsa zuwa Arewa ta tsakiya da kudu maso yamma

Uwargidan shugaban kasar ta bayyana cewa wasu maza sun bata kunya domin a maimakon su yaki wadannan mutane biyu sai su bi dare su je rokon alfarma a wurinsu.

Ta kuma yi kira ga mata da su tashi tsaye a dama da su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel