2019: Wata kungiya tayi zargin cewa akwai jigogin APC da ke adawa da tazarcen Buhari

2019: Wata kungiya tayi zargin cewa akwai jigogin APC da ke adawa da tazarcen Buhari

- Wata kungiya mai rajin goyon bayan jam'iyyar APC ta ce tagano wasu jigogin jam'iyyar da ke adawa da tazarcen shugaban kasa Buhari

- Kungiyar tayi ikirarin cewa jigogin APCn sun kammala shirye shiryen ficewa daga jam'iyyar kafin zabukan 2019

- Shugaban kungiyar ya bukaci shuwagabannin jam'iyyar APC na kasa da su gaggauta daukar matakai na baiwa wadannan jigogi kunya

Kungiyar 'The All Progressives Congress (APC) Solidarity Group', reshen jihar Ondo ta yi ikirarin cewa akwai wasu jigogin jam'iyyar a jihar da ta gano suna kulla makirci don dakile shugaban kasa Muhammadu Buhari daga yin tazarce a babban zaben 2019.

Gbenga Bojuwomi, shugaban kungiyar a jihar ya yhi wannan zargin a lokacin da yake xantawa da manema labarai a sakatariyar APC ta kasa a ranar Talata, 03 ga watan Disamba, a Abuja.

Ya ce kungiyar zuwa yanzu na da kwararan hujjoji na wannan zargi nata. Ya kuma ce ba sau daya ba sau biyu ba, jigogin jam'iyyar ke gudanar da taron sirri kan wannan kuduri nasa kuma suna aikiwa wata jam'iyyar hamayya.

KARANTA WANNAN: Babu wata tsiya da mulkin PDP ya tsinanawa Legas a cikin shekaru 16 - Ambode

2019: Wata kungiya tayi zargin cewa akwai jigogin APC da ke adawa da tazarcen Buhari

2019: Wata kungiya tayi zargin cewa akwai jigogin APC da ke adawa da tazarcen Buhari
Source: Facebook

"Haka zalika, muna amfani da wannan damar wajen sanar da shugaban kasarmu Muhammadu Buhari da shuwagabannin APC na kasa da su gaggauta daukar mataki tun kafin wadannan mutane su sa jam'iyyar cikin kunya," a cewarsa.

Shugaban kungiyar ya ce tuni jigogin jam'iyyar suka kammala shirye shirye na ficewa daga jam'iyyar kafin zabukan watan Janairu na 2019, yana mai cewa "ya kamata shuwagabannin jam'iyyar na kasa su tashi tsaye haikan don ganin sun kunyatar da wadannan mutane."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel