Ku taimakawa mijina ya yi tazarce - Aisha Buhari ta roki mata

Ku taimakawa mijina ya yi tazarce - Aisha Buhari ta roki mata

Aisha, uwargidan shugaban kasa, a ranar Talata, 4 ga watan Disamba ta bukaci yan Najeriya da su taimaka su tabbatar sun dawo da Muhammadu Buhari da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mulki a zaben 2019.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Aisha ta roki matan a lokacin da ta halarci taron shugabannin mata na kasa wanda wata kungiyar siyasa ta shirya domin Buhari da Osinbajo a cibiyar ci gaban mata da ke, Abuja.

Ku taimakawa mijina ya yi tazarce - Aisha Buhari ta roki mata

Ku taimakawa mijina ya yi tazarce - Aisha Buhari ta roki mata
Source: Depositphotos

Rahoton ya bayyana cewa daraktan labaran Aisha, Suleiman Haruna, yace uwargidan shugaban kasar ta bayyana cewa a zaben da ya gabata mata ne suka jajirce wajen zabar APC.

Ta bayyana cewa hakan ne dalilin da yasa gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta samar da wani shiri don tallafawa mata da yaransu domin a rage yawan talauci a tsakaninsu.

KU KARANTA KUMA: 2019: Atiku zai garzaya da kamfen dinsa zuwa Arewa ta tsakiya da kudu maso yamma

Da ta nemi ayi shiru na minti guda domin karrama sojojin da suka rasa rayukansu wajen tsaron kasar, Aisha ta bukaci gwamnati da ta saki hakkokinsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel